Rundunar Ƴan sandan babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja ta karyata raɗeraɗin da ake watsawa wai ƴan ta’adda sun daddasa bamabamai a birnin tarayyar Najeriya.
” Babban abin takaici shine yadda aka rika watsawa a shafukan jaridun kasar nan da na sada zumunta wai an daddasa bamabamai a ko ina a Abuja.
“Ba na jin zai yi wa kasarmu wani amfani a ci gaba da yada irin wadannan jita-jita masu ban tsoro don kara haifar da firgici da ruɗani ga ‘yan kasa da mazauna babban birnin tarayya Abuja da ma Najeriya baki daya,”
Kakakin rundunar Olumuyiwa Adejobi yabkara da cewa babu wani abu mai kama da haka da aka saka a garin Abuja, saboda haka duk mazauna garin Abuja su yi watsi da wannan jita-jita, kowa ya ci gaba da al’amuran sa.
” Ga dukkan alamu akwai yiwuwar wasu ne da ba su nufin kasar nan da alkhairi, suka ƙirkira wannan abu da rana tsaka dinnkawai su tada hankulan mutane
Idan ba a manta ba kasashen Amurka da Birtaniya sun sun fitar da sanarwar bada gargaɗi ga musamman ƴan ƙasashen dake zama a Abuja su rika takatsantsan da zirga-zirgar su a garin.
Sai dai kuma daga baya, gwamnatin Najeriya ta fidda sanarwar cewa jami’an tsaro na ci gaba da bincike da kuma tabbatar da hakan bai auku ba.
Discussion about this post