Ɗan takarar shugaban kasa na NNPP Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa bincike ya nuna musu cewa taron da wasu kungiyoyin Arewa suka shirya za a yi da ƴan takarar shugaban kasa makarkashiya ce ake so a shirya.
Kakakun Kwankwaso ya Abdulmumini Jibrin ya ce ba su su halarci irin wannan taro ba.
” Bayan mun yi bincike mai zurfi game da maƙasudin shirya wannan taro da kungiyoyin Arewa suka shirya, mun gano cewa an shirya wata maƙarkashiya ce domin a ƙaƙaba wa ƴankin Arewa ɗan takara ɗaya dole.
” A dalilin haka muka ga ya dace mu cire kan mu daga wannan taro domin ba adalci aka shirya ba.
” Muna da sahihan bayanai a hannunmu da ke nuni cewa an yi wa wasu mutane ‘tuwo a kwarya’ kuma wadannan mutane sun kammala shiri tsaf na mayar da taron ya zama dandalin amincewa da wani dan takara,”
” A dalilin haka muka ba ba a yi adalci ba idan da karfin tsiya aka ƙaƙaba wa Arewa ɗan takara ɗaya da za su zaɓa, ganin akwai ƴan takara da dama daga Arewa dake takarar kujerar.
” Sannan kuma da mun samu labarin cewa da gangar aka canja ranar taron domin yayi daidai da rabar da wani ɗan takara zai zo Kaduna Kamfen, duk waɗannan mun samu bayanan su daga majiya mau tushe. Sannan shi kansa wannan taro da za ayi wannan ɗan takara ne ya ɗauki nauyin sa.
Sai dai kuma sakataren kungiyar ACF, Murtala Aliyu ya ƙaryata korafin Kwankwaso inda ya ce babu wani ɗan takara da ya gansu game da wannan taro.
” Idan Kwankwaso da makarrabansa na da hujjojin su a rubuce su fito su bayyana su a fili. Ƙungiyoyin shida da suka shirya wannan taro suka haɗu suka tara kuɗin da za su gudanar da wannan taro, babu wanda ya basu kuɗi.
Discussion about this post