Gungun wasu ‘yan APC sun nemi a tsige Gwamna Yahaya Bello daga jagorancin bataliyar matasan kamfen ɗin Bola Tinubu.
Ƙungiyar mai suna ‘Presidential Support Council’, ta ce a cire Yahaya Bello na Jihar Kogi, saboda bai goyi bayan a maida mulki kudancin Najeriya ba, a lokacin da ake takarar zaɓen fidda gwani.
Yahaya Bello na cikin ‘yan takarar da ba su janye wa Bola Tinubu ba. An gwabza ya samu ƙuri’u 47 daidai da yawan shekarun sa a duniya.
Bello na sahun gaba na wadanda suka riƙa kamfen cewa matashi ne ya kamata ya yi mulki a 2023, ba tsoho kamar Tinubu ba.
An naɗa shi a yanzu ya zama Kodinatan Matasan Kamfen ɗin Bola Tinubu na Ƙasa a yaƙin neman zaɓen 2023.
Sai dai kuma shugaban gungun masu ƙorafin mai suna Kassim Mohammed, ya kira taron manema labarai a ranar Litinin. A wurin taron ya ce matsayar da Yahaya Bello ya ɗauka cewa bai yarda mulki ya koma kudu ba, dalili ne na rashin ya cancanci jagorancin kamfen ɗin matasa na ƙasa baki ɗaya.
Cikin watan Yuni Bello ya ƙi amincewa da sunayen ‘yan takarar kudu su biyar da Gwamnonin APC su ka bayar domin a fitar da ɗaya a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa.
Kassim Shettima ya ce Yahaya Bello mai shekaru 47 a duniya ba matashi ba ne, bai kamata a ba shi jagorancin ƙungiyar matasa ba.
“Lokacin sayar da fam na takara, APC ta rage kashi 40 cikin 100 na kuɗin fam ga matasa. Amma Yahaya Bello naira miliyan 100 ya biya ya sayi fam na takara, ba naira miliyan 60 yadda matashi ya kamata ya biya ba.
“Hakan ya nuna cewa ita kan ta APC ba ta ɗauke shi a matsayin matashi ba. Da matashi ne naira miliyan 60 za ta karɓa a hannun sa, ba naira miliyan 100 ba,” cewar Kassim Mohammed.
Haka kuma Mohammed ya koka ganin babu matasa a cikin zaratan rundunar kamfen ɗin TInubu ta mutum 422.
Ya ce tilas sai an bai wa matasa guraben bayar da ta su gudummawar idan ana so a yi nasara.
Discussion about this post