Rundunar Yaƙin Neman Zaɓen Atiku Abubakar ta ƙaryata zargin da Gwamnatin Tarayya ta yi cewa wai Daftarin Ceto Tattalin Arzikin Najeriya na Atiku 2023, kwafo shi PDP ta yi daga daftarin APC.
A ranar 14 Ga Satumba ce Atiku ya ƙaddamar da daftarin, wanda Ministan Yaɗa Labarai Lai Mohammed ya yi masa martanin cewa ba komai a ciki sai bulkara da hauragiya kawai.
Ministan ya ce Daftarin Atiku bai bijiro da wani sabon abu kan batun samar da aikin yi ba da sauran hanyoyin bunƙasa ƙasa.
Sai dai kuma rundunar kamfen ɗin Atiku ta sake yin martani a ranar Alhamis, inda ta ce ƙoƙarin kwatanta daftarin Atiku da hauragiyar da APC ta yi tsawon shekaru bakwai da sunan ayyuka, ai almara ce kawai Minista Lai Mohammed ke yi.
“Kalaman Lai Mohammed ai rainin hankali ne ga Atiku da kuma ‘yan Najeriya baki ɗaya.
“Saboda wannan gwamnati ta hau mulki ba tare da wata fallen takarda ko da guda ɗaya mai ɗauke da daftarin tsare-tsaren yadda za ta ceto ƙasar nan da tattalin arzikin ta ba.”
Daga nan sai PDP ta fara da tunatar da APC cewa, “saboda tsakanin rashin shiri fa sai da aka shafe watanni shida kafin gwamnatin APC ta naɗa ministoci. Shin wannan ma duk cikin daftarin ceto tattalin arzikin ne?”
Daga nan kuma rundunar kamfen ɗin ta Atiku ta nemi Lai Mohammed ya nemi afuwar ‘yan Najeriya.
Wannan raddi na PDP, martani ne ga Lai Mohammed, wanda ya fara maida wa Atiku raddi, yayin da ya ce ”Idanun tattalin arzikin Najeriya garau su ke, ba su fama da dundumi”, kamar yadda Atiku ya yi zargi.
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa furucin da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar ya yi cewa tattalin arzikin Najeriya na fama da ciwon dundumi, kuma gab ya ke da makancewa, ba gaskiya ba ce, farfaganda ce kawai don ya razana jama’a.
Atiku ya yi wannan iƙirarin na durƙushewar tattalin arzikin Najeriya, a lokacin da ya ke gabatar da Daftarin Ceto Tattalin Arzikin Najeriya da zai yi kamfen ɗin takarar shugaban ƙasa da shi, kwanan baya, a Legas.
A lokacin ƙaddamarwar ce har Atiku ya ce idan aka zaɓe shi a 2023, to a cikin kawanakin 100 na farkon shugabancin sa zai danƙara Naira tiriliyan 10 cikin tattalin arziki, lamarin da ya janyo masa raddi, ana tambayar sa inda zai samo kuɗaɗen.
A martanin da Ministan Yaɗa Labarai Lai Mohammed ya mayar wa Atiku, a wurin taron manema labarai a ranar Alhamis a Abuja, ya ce tabbas Najeriya na fuskantar ƙalubalen tattalin arziki, amma maganar a ce wai tattalin arzikin ya kusa durƙushewa ko kuma a yi masa kallon idanun da su ka kusa makancewa, ƙarya ce, ba gaskiya ba ce.
“Tattalin arzikin Najeriya bai kusa durƙushewa ba, tattalin arzikin Najeriya kamar tofa ya ke, ya yi juriya sosai, domin a 2016 da 2020 ya tsallake siraɗin durƙushewa.”
Lai ya ci gaba da bayyana irin dajin da tattalin arzikin Najeriya ya keto a ‘yan shekarun nan, da kuma yadda ya farfaɗo albarkacin wasu nagartattun tsare-tsare da gwamnatin tarayya ta bijiro da su.
Sannan kuma Lai Mohammed ya ƙaryata zargin da Atiku ya yi cewa tun da APC ta kafa gwamnati cikin 2015, “a duk shekara sai an samu giɓi cikin kasafin kuɗi.”
“Zargin Atiku ba gaskiya ba ce. Ba daga 2015 ne aka fara samun giɓi cikin kasafin kuɗi ba. An fara samun wannan giɓin tun cikin 2009, lokacin da ma ake sayar da gangar ɗanyen mai guda ɗaya dala 100.”
Daga nan kuma Lai Mohammed ya riƙa lissafa irin manyan ayyukan da Gwamantin Tarayya ta yi a faɗin ƙasar nan, inda ya ƙarƙare da cewa “surutan da Atiku ya yi, ai ba wani sabon abu ya faɗa ba.”
Discussion about this post