Kwamishinan tsaron jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya yi kira ga mataya dake jigila a hanyar Kaduna-Abuja cewa gwamnati na kokarin ganin an kawo karshen cinkoson da matafiya ke fuskanta a wannan hanya.
Aruwan ya ce’ Yanzu haka muna tattaunawa da kamfanin Julius Berger da sauran masu ruwa da tsaki da ke aikin hanyar, don ganin an warware matsalar da yake kawo tsanani ga matafiya a wannan hanya.
Matafiya na afkawa cikin tsananin wahala a cikin makonnin nan a dalilin dagargajewar hanyar da motoci ba su iya bi cikin kwanciyar hankali. Tafiyar awa 2 sai a yi awa 6 ana fafatawa a wannan hanya.
Wani matafiya da ya tattauna da PREMIUM TIMES Hausa, ya bayyana cewa hanyar ta zama kamar ba hanyar mota daga Kaduna zuwa Abuja ba.
” Haba ace wai hanyar da ta hada Arewa da Kudancin Kasarnan duk bata wuce kilomita 200 amma ta gagari gwamnatin Najeriya shekara 8 kenan sai alkawari ake yi. Idan aikin ba zai yiwu da wuri ba, ai sai a dan rika yi wa hanyar faci akai akai kamar yadda gwamnatocin baya ke yi kafin a cigaba da gyaran.
” Hanyar ta yi munin da yanzu ma da kyar ake iya binta, ba a iya bi kuma hanya ce da mutane da dama ke cin abinci akai. Ba sai lallai an gyara ba, a dan yi faci faci zuwa lokacin da gyarar zai dawo gadangadan mana, tsakani da Allah.
Discussion about this post