Hukumar NDLEA ta sake maka dakataccen babban jami’in ɗan sanda Abba Kyari a kotu, bayan ta gano wasu maka-makan gidaje da ya mallaka a Maiduguri da Abuja.
Hukumar ta ce cikin gidajen har da rukunin gidaje sukutum, wato estate da kuma gingima-gingiman kantinan hada-hadar zamani, wato Plazas.
Kyari wanda ya daɗe tsare a kurkuku tun bayan da NDLEA ta kama shi bisa zargin safarar muggan ƙwayoyi, yanzu haka hukumar ta ƙara maka shi kotu bisa dalilin waɗannan kadarori da kuɗaɗen da aka gano a hannun sa.
Baya ga naira miliyan 207 da aka gano a wasu asusun ajiyar sa na bankunan GTB, UBA da Sterling, an kuma gano fam na Ingila har 17,598.
NDLEA ta maka shi kotu ana tuhumar sa da laifin ɓoye wa gwamnati adadin yawan kadarorin da ya mallaka, wanda babban laifi ne ga ma’aikacin gwamanti ya aikata haka.
An kuma gano ashe ya mallaki wani filin wasan ƙwallon dawakai, maka-makan gonaki da sauran kadarori da dama.
A wannan ƙarar dai tuhuma 24 ce ake yi masa, kamar yadda Daraktan Gurfanar da Masu Laifi Kotu na NDLEA, Joseph Sunday ya shigar a kotu.
A ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CR/408/22, ana tuhumar Abba Kyari ne tare da wasu ƙannen sa biyu, Mohammed Kyari da Ali Kyari.
Discussion about this post