Ɗan takarar sanata na Yobe ta Arewa Bashir Machina ya ƙaryata wasikar da ake yaɗawa wai ya janye daga takarar kujerar sanatan Yobe ta Arewa.
A wasikar da aka rika ƴadawa wai ta fito daka wurin sa na kunshe sa cewa wai ya janye daga takarar sanatan Yobe ta Arewa sannan kuma ma ya fice daga jam’iyyar APC.
Machina ya karyata hakan ya na cewa wasu ne kawai suka fidda wannan wasika ta karya domin wata muguwar manufa tasu.
” Ni ban janye daga takara ba sannan ban fice daga APC ba. Ina nan daram dam a APC kuma da ni za a fafata a zaben 2023.
Bayan haka akwai rahotannin da suka nuna cewa hukumar zaɓe ta kai ƙarar cewa zaɓen fidda gwani wanda dakanta ta gudanar cewa ba ayi bisa ka’ida ba.
Tun bayan faduwa zaɓen fidda gwani da shugaban majalisar Dattawa Ahmed Lawan yayi a zaben APC na shugaban kasa aka fara yi wa Machina bita da Kullin dole ya janye daga takarar sanata da ya ci ya mika wa Ahmed Lawan wannan kujera.
Machina ya ce ba zai janye ba ko kuma ya mika wa Lawan kujerar takarar cewa ya kamata a bari wani ya tafi majalisar domin Ahmed Lawan ya daɗe a wannan kujera.
Discussion about this post