Ɗan takarar shugaban ƙasa a PDP, Atiku Abubakar, ya ƙara jaddada cewa zai taimaka wa ƙabilar Igbo su yi shugabancin Najeriya, idan har aka zaɓe shi 2023 kuma ya kammala wa’adin sa kan mulki.
Atiku ya sha wannan alwashin a taron sa da shugabannin PDP na yankin Kudu maso Gabas da aka yi a Inugu ranar Talata.
Ya ce ƙabilar Igbo nagartattun mutane ne, shi ya sa ma a takarar da ya yi 2011 da 2019 ya ɗauki Igbo matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa.
Ya ce yanzu ma a karo na uku kenan ya sake ɗaukar ɗan ƙabilar Igbo matsayin mataimakin takarar shugaban ƙasa na PDP a zaɓen 2023.
“To don me za ku ce ba zan ba ɗan ƙabilar Igbo mulki ba bayan kammala wa’adin mulki na idan aka zaɓe ni?
“Na daina kiran ku maza da mata, sai dai na kira ku ‘yan uwa na maza da mata. Na tabbatar kuma ba za ku bari na kasa yin nasara ba, ganin yadda na ke matuƙar ƙaunar ku.” Inji Atiku.
Atiku ya ce ko a baya ya sha goyon bayan yan Kudu maso Gabas da su ka fito takara har ta mataimakin shugaban ƙasa da ta shugaban ƙasa.
Daga nan ya yi ta lissafa alƙawurran da su ka haɗa har da inganta ilmi da kawo ƙarshen yajin aikin malaman jami’o’i.
Baki Shi Ke Yanka Wuya:
‘Wanda zai yi min mataimaki shi zai gaje ni idan na hau mulki’ -Atiku
Tun a ranar 16 Ga Yuni, ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyyar PDP Atiku Abubakar ya bayyana cewa idan ya samu nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, to mataimakin sa ne zai gaje idan zai sauka.
Atiku ya bayyana haka ne a cikin jawabin sa lokacin da ya ke bayyana sunan Gwamnan Jihar Delta Ifeanyi Okowa a matsayin mataimakin takarar sa.
A cikin jawabin, Atiku ya ce ba ya tsoron ɗaukar kasada, shi ya sa na ɗauki Gwamna Okowa mataimakin takara.
Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyyar PDP Atiku Abubakar ya bayyana dalilan da su ka sa ya ɗauki Gwamnan Jihar Delta Ifeanyi Okowa ya yi masa takarar mataimakin gwamna a zaɓen 2023.
“Na yanke shawarar zaɓar mataimakin takara ne wanda tilas ya san irin halin taɓarɓarewa da lalacewa da rugu-rugun da gwamnatin APC ta yi wa wannan ƙasar.” Inji Atiku.
Atiku Abubakar ya zaɓi Ifeanyi Okowa domin kamar yadda ya ce wanda zai ɗauka tilas zai kasance ya na da masaniyar muhimmancin ilmi a cigaban zamani cikin al’umma, ta yadda za mu shirya matasa su riƙa yin gogayya da sauran ƙasashen duniya a zamanance.”
Sauran dalilan da ya lissafa sun haɗa da wanda ya ke da shauƙin ganin an ƙara haɗa kan Najeriya, kuma wanda zai taimaka masa a samu wannan nasarar.
Atiku ya nuna farin cikin yadda aka gudanar da zaɓen fidda gwani lafiya, kuma ya gode wa sauran ‘yan takarar da ya kayar, tare da sake neman haɗin kan su domin a tafi tare har a kai ga nasara.
“Kuma ina farin ciki da alfaharin fatan cewa idan na samu masarar zama shugaban ƙasa, to mataimaki na ne zai gaje ni. Don haka ya zauna da shirin shi ma Shugaba ne mai jiran gado.
“Kuma mataimakin takara ta zai kasance wanda a shirye ya ke ya taimake ni mu kawo ƙarshen matsalar tsaro a faɗin ƙasar nan.”
Atiku ya ce tilas mataimakin sa zai kasance wanda zai taya shi dawo da ɗimbin masu zuba jari daga waje waɗanda su ka gudu daga ƙasar nan, yayin da gwamnatin APC ke barci har ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga masu ƙaryar su makiyaya ne su ka addabi ƙasar nan, da manoma da makiyayan ainihi.
Atiku ya ce ya saba ɗaukar matsayi mai wahala sosai. Don haka a yanzu ma sai da ya tsaya ya darje, bayan ya tuntuɓi manyan masu ruwa da tsaki sosai, sai ya ɗauki Ifeanyi Okowa.
Atiku ya ce a yanzu ba lokacin tsayawa surutai ba ne, jan aikin da ke gaban su shi ne tabbatar da cewa an yi nasara a zaɓen 2023.
Discussion about this post