Wasu Fulani masu cin Kasuwa sun tada rikici a kasuwar mako-mako ta Tegina dake karamar hukumar Rafi jihar Neja a dalilin kokuwar mallakar budurwa.
Rikicin ya dauko asali ne tun a ranar Juma’ar makon jiya a lokacin kasuwa ta cika ana ta hadahadar kasuwanci sai ga gungun matasan Fulani da ‘yan matan su sun shigo don yin siyayya da kuma cigaba da shagulgulan sallah.
Ana cikin haka ne sai daya daga cikin bangaren Fulanin ya yi kokarin yin kwacen wata budurwar da ba tasa ba.
A dalilin haka ne fa sai rikici ya barke inda mutane da masu shaguna duk suka gudu daga kasuwar.
Wani mazaunin kauyen Hassan Muhammad ya ce ‘yan sanda na mobal dake kauyen suka kawo dauki ta hanyar harba bindiga sama da kama wasu daga cikin Fulanin.
Muhammad ya ce wadanda suka ji rauni an garzaya dasu asibiti ana duba su.
Idan ba a manta ba Tegina itace garin da ‘yan bindiga suka sace daliban makarantar Islamiya 136 a shekarar 2021.
‘Yan bindigan sun sako daliban ne bayan iyayen su sun biya wuri na gugan wuri har naira miliyan 60 da baburan hawa biyar.
Tegina na da iyakan ƙasa da karamar hukumar Maru dake jihar Zamfara da Birnin Gwari dake jihar Kaduna wanda suma sun yi kaurin suna wajen fuskantar hare-haren yan bindiga.
Discussion about this post