Wani binciken kwakwaf da PREMIUM TIMES ta yi ya bankaɗo yadda ma’aikatat Addinin Musulunci na jihar Barno ya karya doka wajen wawushe kuɗin ma’aikatar don siyan ragunan sallah ga mutanen jihar, wanda har yanzu ba su ga ko ƙaho ba tun 2019.
Sai dai kuma babu wanda ya ga ko ƙaho cikin talakawa a jihar.
Rahoton ‘Oditon’ jihar ya nuna cewa ba a bi foka ba wajen kamfatar waɗannan kuɗaɗe sannan kuma babu tabbacin an soya ragunan kamar yadda takardar bayanin yadda aka kashe waɗannan kuɗaɗe bayan an kamface su.
Wakilin PREMIUM TIMES ya tattauna da mazauna jihar game da rabon ragunan a 2019 da ma’aikatar addinin musulunci na jihar ta yi sun ce ba su ga ko kaho ba ballantana su yi tunanin naman sallah.
” Mu fa ba mu iya siyan rago, shinkafar Sallah ma da kyar nake iya siyan sa. Babu wanda ya raba mana nama ko ragon Sallah a 2019 wai daga gwamnati.
Haka mazauna garin Maiduguri da dama suka shaida wa PREMIUM TIMES.
Kakakin gwamnatin jihar Gusau, ya shaida wa wakilin mu cewa gwamna Babagana Zulum bai san da wannan harkalla ba.
” Idan dai gwamna Zulum ne, kowa ya san shi cewa babu wanda ya isa yayi wa kuɗin gwamnati hawan kawara, ko kuma ya kashe su ba tare da an bi doka ba.
” Kuma ku sani cewa ma’aikatu na da yawa a jihar saboda haka ba duka bane gwamna zai san diddigin yadda suke kashe kuɗaɗen. Amma kuma idan rahotan binciken ya kai teburin gwamna dlza a bi diddigin abin.
Discussion about this post