Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya aika wa ‘yan bindigan da suka kai hari Shiroro da kakkausar martani in da ya ce kwanakin su a kirge suke domin jami’an tsaro na tafe su gama da su.
An tabbatar da kisan mutum 43, waɗanda su ka haɗa da sojoji 30 da mobal 7, an kuma tabbatar da ɓacewar wasu jami’an tsaron a gumurzun su da ‘yan ta’adda a daji haƙar ma’adinan da ke Ajata-Aboki, cikin Ƙaramar Hukumar Shiroro a Jihar Neja.
Mazauna yankin Shiroro a ranar Alhamis ce su ka shaida wa wakilin mu yadda ‘yan bindiga su ka yi wannan mummunar aika-aikar a ƙazamin harin da aka kai ranar Laraba.
Waɗanda su ka ga irin yawan zugar ‘yan ta’adda a kan babura ɗauke da zabga-zabgan makamai su ka ratattaki dandazon wurin da ake haƙar ma’adinan, su ka kashe farar hula, sojoji, mobal da kuma arcewa da wasu mutanen da su ka haɗa har da ‘yan ƙasar Chana.
Kakakin Gamayyar Ƙungiyoyin Raya Garin Shiroro mai suna Salisu Sabo, ya ce ba a yi zaton za a kai harin ba, saboda yankin ya shafe watanni ba a ji motsin an kai masa hari ba.
Ya ce su na zaune lafiya bayan da aka girke sojoji a yankin.
Sabo ya ce kafin ‘yan ta’addar su kai ga wurin haƙar ma’adinan, sai da su ka keta ƙauyuka da dama.
Sabo ya ce an ce maharan sun riƙa kwantar wa mazauna ƙauyukan hankula, su na ce masu kada wanda ya gudu, ba su aka zo kai wa hari ba.
An ce sun bindige wani mutumin ƙauye bayan sun tambaye shi hanyar da wurin haƙar ma’adinan, amma ya tsaya ya na yi masu dawurwura.
“Yan bindigar dai an tabbatar cewa Boko Haram/ISWAP ne. Da ganin su za ka san cewa ba ‘yan Najeriya ba ne. Su na da dogon gashin gashi a zai, ga kuma huda hancin su.
“Sun wuce su na ambaton Allah, Allahu Akbar!”
Sun rabu gida huɗu. Su na sanye da rigunan sojoji, ‘yan sanda, har da na ‘yan sakai.
“Su na isa ma’dinar kawai sai suka kwashi mutanen da su ka yi garkuwa da su, daga nan su ka buɗe wuta.”
“Da su ka isa Unguwar Maji da ke Mazaɓar Erena, a can ne su ka yi arangama da sojoji.
“Sojoji da maharan sun yi gumurzun da tun wajen 4 na yammaci, amma har washegari ranar Alhamis da safe mu na jin rugugin bindigu.”
Ya ce baya ga tulin jami’an tsaron da aka kashe, har yanzu wasu sun ɓace babu labarin su.
” Ku sani duk inda kuka saka kan ku, ko da ko a karkashin ina ne, za mu zo mu iske ku kuma sai kun yaba wa aya zaki. Babu gudu ba ja da baya. Sai mun bi wa mutanen Shiroro hakkin su.