Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa zaɓin Kashim Shettima da ɗan Takarar APC Bola Tinubu yayi zaɓi ne mai kyaun gaske.
A hira da yayi da talbijin Arise, Kwankwaso ya ce ” Na dade ina mu’amala da Tinubu, kuma shi mutum ne mai zurfin tunani da hangen nesa sannan ya da sanin ya kamata.
” Zaɓen Shettima da yayi ya yi daidai matuka domin mun yi aiki da Shettima lokacin ina gwamna shima yana gwamna kuma shi mutum ne mai natsuwa da kwazo.
Idan ba a manta ba, Tinubu ya bayyana Kashim Shettima a matsayin mataimakin sa a takarar shugaban kasa da ke tafe.
Discussion about this post