Wasu daga cikin ƴan jam’iyyar APC mazauna garin Kaduna sun nuna rashin jin daɗin su da ɗan Takarar shugaban kasa na jam’iyyar bai zaɓi gwamnan jihar Nasir El-Rufai ɗan takarar mataimakin shugaban kasa ba.
Tun bayan da Bola Tinubu yayi nasara a zaɓen Fidda gwani na jam’iyyar APC ake ta ayyana sunayen wasu jigajigan ƴan jam’iyyar da suka haɗa da gwamna El-Rufai wanda zai zaɓa ɗan takarar mataimakin sa.
Baya ga shi El-Rufai din wasu sun yi zato ko kuma kila ɗaya daga cikin gwamnonin APC ne zai zaɓa mataimakin sa.
Yin bu a garin Daura ranar Lahadi ya sanar wa shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa ya zaɓi Kashim Shettima ne a natsayin ɗan takarar mara makin shugaban kasa wanda zasu yi mulki tare idan Allah ya bashi nasara a zabe mai zuwa.
Sai dai kuma wasu da dama musamman waɗanda suke ƙaunar Nasir El-Rufai sun nuna rashin jin daɗin su ga zaɓin Shettima da Tinubun yayi.
” Kai bannji daɗi ba Amma kuma haka Allah ya Duk da naso ace shine ɗin Tinubu ya zaɓa babu komai za mu ci gaba da yi masa aiki domin samun nasarar jam’iyyar a 2023.” In ji wani mazaunin Kaduna.
Hakan nan ita ma Hawwa Baba , ta ce ” Na fi ganin kamar El-Rufai shine zai fi dacewa da ya zama mataimakin Tinubu, amma kuma shi Tinubu ya fi mu sanin dalilin da ya sa ya bar El-Rufai ya zabi Shettima.
Sai dai kuma dukkan wanda suka tattauna da PREMIUM TIMES HAUSA, sun bayyana cigaba da baiwa APC goyon baya, 100 bisa 100 har ta gai ga nasara a 2023.
Discussion about this post