Shugaban Sashen Daƙile Safarar Muggan Ƙwayoyi na Hukumar NDLEA, Patricia Afolabi, ta bayyaana wa Babbar Kotun Tarayya a ranar Litinin yadda ta yi gwajin bin-diddigin yadda ta gano cewa shaidar hodar Ibilis ɗin da NDLEA ta gabatar a kotu, ta biyo ta hannun Abba Kyari.
Ana tuhumar Kyari da wasu mutum huɗu da laifin harƙallar hodar Ibilis tsakanin 19 Ga Janairu zuwa 22 Ga Janairu, 2022.
Afolabi ta ce laifin da su Kyari su ka aikata ya saɓa wa Dokar NDLEA ta 11(c).
Tuni dai biyu daga cikin waɗanda ake tuhuma tare da Kyari su ka amsa laifin su ba tare da yi wa Mai Shari’a ja-in-ja ba. Hakan ya sa aka ɗaure kowanen su shekaru biyu a kurkuku, saboda ba su wahalar da kotu ba.
Yayin da aka fara shari’ar Kyari da sauran waɗanda ake tuhumar su biyu a ranar Litinin, Afolabi a matsayin ta na mai gabatar da ƙara da kuma gabatar da shaida, ta ce wa kotu cewa gwajin da aka yi wa abin da aka samu a hannun Kyari da sauran mutanen biyu, shaidu 21 ko hujjoji 21 da mai gabatarwa ya gabatar sun tabbatar da cewa hodar Ibilis ce aka samu a hannun su.
Ta ce a ranar 7 Ga Fabrairu, 2022 ta karɓi aikin gwajin daga hannun jami’in gwaji Abubakar Aliyu, waɗanda fakitin ledoji ne wadda kowace ke ɗauke da kwali ko sunƙi 24.
Daraktan Shigar da Ƙara na NDLEA Sunday Joseph ne ya gabatar da Afolabi a kotu domin gabatar da shaidu.
Lauyan waɗanda ake ƙara ya tabbatar da tabbacin shaidu kayan mayen da lauyan NDLEA ya gabatar wa kotun. Sunan lauyan waɗanda cake ƙara dai Emeka Nwete.
Da ta ke amsa tambayoyin lauyan Kyari mai suna Onyechi Ikpeazu (SAN), Afolabi ta shaida wa kotu cewa ba tilas ba ne sai a gaban wanda ake tuhuma ake yin gwaji.
Ta ce ba dole ba ne sai a gaban wanda ake tuhuma za a yi gwajin.
Za a ci gaba da shari’ar ranar 29 Ga Agusta, inda za a yanke hukuncin ko a aika da Abba Kyari ga mahukuntan Amurka ko ba za a aika da shi ba, kamar yadda Mai Shari’a Inyang Ekwo ya bayyana.
Salsalar Yadda ‘Hayaƙin Hodar Ibilis’ Ya Buwayi Kyari da Kotun Tarayya:
A farkon fara shari’ar ne dai dillalan hodar sun amsa laifin su, Kyari da sauran ‘yan sanda ba su amsa laifi ba.
Waɗanda ke cikin zauren shari’ar da aka fara ta su Abba Kyari a Babbar Kotun Tarayya, Abuja, sun cika da mamaki, yayin da mutum biyu da ake zargin sun shigo da hodar ibilis daga Brazil da Habasha, su ka amsa laifin su, ba tare da wata jayayya ba.
Chibunma Patrick da Emeka Alphonsus Ezenwanne sun amsa laifin tuhuma mai lamba ta 5, 6 da na 7, waɗanda duk ke da nasaba da laifin shigo da muggan ƙwayoyi.
“Ran Mai Shari’a Ya Daɗe, na aikata laifin.” Haka kowanen su ya sanar wa kotu a ba’asin su da aka shigar daban-daban.
An karanta masu cewa sun karya dokar Hukumar NDLEA, ta Sashe na 14(b), ta 30 a ƙarƙashin Dokar 2004.
An tuhume-tuhume su da shigo da koken a filin jiragen sama na Akanu Ibiam da ke Enugu, a ranar 25 Ga Janairu, 2022.
PREMIUM TIMES ta bada labarin NDLEA sun gurfanar da Abba Kyari a kotun Abuja.
Jami’an Hukumar NDLEA sun gurfanar da dakataccen Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda, Abba Kyari a Babbar Kotun Tarayya ta Kaduna.
An shiga da shi kotun sa safiyar Litinin misalin ƙarfe 8:12 na safiya.
An gabatar da shi ne bisa zargin sa tare da wasu jami’an ‘yan sanda huɗu da laifin safara da kuma tu’ammali da hodar ibilis mai nauyin kilogiram 22.35.
NDLEA sun kama shi tare da ‘yan sandan huɗu waɗanda su ma ke ƙarƙashin sa a lokacin da ya ke shugaban ‘Yan Sandan Kai Ɗaukin Gaggawa masu kamen ‘yan damfara da garkuwa da mutane.
Kafin NDLEA ta kama shi, Kyari ya shafe watanni shida a dakace, bayan zargin sa da haɗa baki da gawurtaccen ɗan damfara Hushpuppi.
An zarge shi da shirya damfarar dala miliyan 1.1, lamarin da ya janyo Amurka ke neman a tura a can ta yi masa hukunci a Amurka.
A zaman shari’a, su Kyari za su fuskanci tuhumar amfani da kuma mallakar hodar Ibilis ba bisa ƙa’ida ba.
Sannan akwai wata hutuma da ake wa Kyari shi kaɗai, wadda ake zargin sa da bai wa babban jami’in NDLEA toshiyar bakin Dalar Amurka 61,400 don kada NDLEA ta bincika kuma kada ta auna wata hodar Ibilis don kada a gane ko mece ce.
Manyan ‘yan sanda huɗu da ake tuhuma tare da Kyari sun haɗa da Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda Sunday Ubua, Mataimakin Sufurtanda Bawa James, Sufeto Simon Agirgba, Sufeto John Nuhu.
Akwai fararen hula biyu, Chibunma Patrick da Emeka Alphonsus Ezenwane. Su ne ake zargin sun shigo da hodar Ibilis mai nauyin kilogiram 21.35.
A ranar 28 Ga Febrairu ce Kotu Ta Ƙara Hana Belin Abba Kyari:
Babbar Kotun Tarayya a karo na biyu a Abuja, ta ƙi amincewa da belin dakataccen Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda Abba Kyari, wanda a yanzu haka ke ci gaba da kasancewa a tsare a hannun Hukumar Hana Safara da Tu’ammali da Muggan Ƙwayoyi (NDLEA).
NDLEA ta kama Abba Kyari bisa zargi da binciken sa wajen hannun shigo da hodar ibilis mai nauyin kilogiram 25 daga Brazil.
Mai Shari’a Inyang Ekwo dama tun a ranar 21 Ga Fabrairu ya yi fatali da takardar neman belin Kyari da aka ba shi, bisa dalilin cewa Kyari na fama da fama da rashin lafiya.
Ekwo ya umarci masu neman beli su tura wasiƙar ta su ga Hukumar NDLEA, wadda ita ce ke tsare da Kyari, kuma ita ɗin ce ta kama shi.
A wannan Litinin kuma Mai Shari’a Ekwo ya ƙara yin fatali da neman beli, inda ya ce “Ai umarnin da wata kotu ta bayar cewa NDLEA ta ci gaba da tsare Kyari har sai bayan ƙarin wasu kwanaki 14 a tsare.
Ya ce wannan hukunci ya shafe duk wata maganar neman beli a yanzu, domin an bai wa NDLEA damar ci gaba da binciken Kyari da ke a hannun ta.
Daga nan sai Ekwo ya ce sai bayan cikar wa’adin kwanaki 14 da aka ƙara wa NDLEA sun cika, sannan za a zo a yi maganar beli.
“Saboda haka ba zan bayar da belin sa ba.” Inji Mai Shari’a Ekwo.
Da ya koma kan batun rashin lafiyar da lauya ya ce ke damun Kyari, ya umarci NDLEA ta ba Kyari damar ci gaba da shan magungunan ya likita ya amince ya riƙa amfani da su, kamar yadda kotun ta bayar da umarni a ranar 22 Ga Fabrairu.”
Discussion about this post