Bankin Bunƙasa Ƙasashen Afrika ya danƙara wa Najeriya bashin dala miliyan 134 domin haɓɓaka noma da bunƙasa abinci a cikin gida.
A ranar Juma’a ce AfDB ya amince zai bayar da lamunin domin samun nasarar noma wadataccen abinci, a ƙarƙashin shirin Bunƙasa Kayan Abinci da aka raɗa wa suna ‘Agro Pocket’.
A ƙarƙashin shirin ana so a bunƙasa noma kayan nau’o’in abincin da ake sarrafawa a yi abincin sarelel da kuma mai, ta hanyar haɓɓaka ƙoƙarin da kamfanoni ke yi domin samar da tan miliyan 35 a duk shekara.
Haka kuma shirin na ‘Agro-Pocket’ zai samar da ƙarin seralel daga tan 1.42 kowace hekta, zuwa tan biyu a kowace hekta, lokacin kakar Satumba 2022 zuwa Disamba 2023.
Wannan gagarimin shiri ya yi daidai da Tsarin Gaggauta Afrika ta Noma Isasshen Abinci, wanda kuma Najeriya na sahun gaba wajen cimma wannan ƙudiri, domin cike girɓin ƙarancin abincin da yaƙin Rasha da Ukraniya ya haifar a duniya.
Tun farkon kullen korona da aka yi a duniya baki ɗaya ne yakan abinci ke ci gaba da yin tashin-gwauron-zabo a duniya.
Sai kuma aka yi rashin sa’a shekara ɗaya baya yaƙi ya ɓarke tsakanin Rasha da Ukraniya, ƙasashe biyu maƙwauta masu arzikin noma.
Dalilin yaƙin matsalar kayan abinci ta addabi duniya.
Shirin Bunƙasa Abinci a Afrika shiri ne da ya samo rushe da asali daga Shirin Bunƙasa Abinci na Tsawon Shekaru 10, ta hanyar bunƙasa noman da ke jure matsalar canjin yanayi na zafi ko sanyi.
Ana so ne a gaggauta bijiro da shirin tun kafin ƙalubalen matsalolin su danne yawan al”umma, ciki kuwa har da mata da ɗimbin matasa.
Ana kirdado da hasashen cewa yawan al’ummar Najeriya zai kai mutum 402 nan da shekarar 2023, wato shekaru 27 masu zuwa.
Yanzu dai yawan mutane a Najeriya ya kai miliyan 206, kuma ita ce ƙasa mafi yawan jama’a a Afrika, sannan kuma ƙasa mafi yawan baƙaƙen fata a duniya.
Kashi 48 na mutanen Najeriya a karkara su ke, kuma su ne ke noma kashi 90 bisa 100 na kayan abincin da ake nomawa a cikin ƙasa.
Sai dai kuma rashin samun tallafi ya sa akasarin manoma sun fi dogara ne da noman gargajiya, ba na zamani ba.
Hakan na haifar da kasa noma wadataccen abincin ake buƙata a cikin ƙasar.
Discussion about this post