Ƴan bindiga da ake zargin makiyaya Fulani ne sun yi garkuwa da mutum 15 a kauyen Mgbuji, garin Eha-Amufu dake karamar hukumar Isi-Uzo a jihar Enugu.
Bisa ga rahotan da jaridar ‘Punch’ ta buga ‘yan bindigan sun sace da wadannan mutane a hanyar Mgbuji-Agu ranar Litini da misalin karfe 7 na safe.
Wani mazaunin kauyen Onyekachi Odo ya ce maharan sun yi awon gaba da mutanen ne a daidai sun fito za su garzaya gonakin su.
Kakakin kauyen Chijioke Ogbodo Wanda ya sanar da haka ranar Litini ya ce ana fama da sace-sacen mutane ba tare da jami’an tsaron da ake da su sun yi komai a kai ba.
“Mun samu labarin cewa ‘yan bindiga sun afka kauyen mu kuma mun yi gaggawar kiran jami’an tsaro dake Eha-Amufu amma ba su zo ba.
Ya yi kira ga gwamnati da ta gudanar da bincike domin ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Daniel Ndukwe ya ce rundunar bata da cikaken bayanai kan harin.
Hare-haren mahara a Enugu
Kauyen Mgbuji da wasu kauyukan dake garin Eha-Amufu na yawan fama da hare-haren ‘yan bindiga a jihar.
Garkuwa da mutum 15 da aka yi a kauyen Mgbuji ya auku bayan wata daya da ‘yan bindiga suka kashe mutum uku a kauyen.
A cikin wannan watan ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutum bakwai sannan suka kashe mutum uku a wata kauye.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Abubakar Lawal tare da wasu manyan jami’an tsaro sun ziyarci kauyen sannan sun yi wa mutane alkawarin cewa za su dauki mataki don dakile hare-haren ƴan bindiga a jihar.
Discussion about this post