Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa har yanzu bai cimma matsaya ba game da wanda zai ɗauka yayi masa takarar mataimakin shugaban kasa ba.
Tinubu ya faɗi haka ne a lokacin da yake jawabi a wurin taron bukin murnar cika shekaru 60 da kakakin majalisar tarayya, Femi Gbajabiamila yayi a Abuja.
Tinubu ya ce ” Akwai lokacin da na kusa barkewa da kuka saboda Gbajabiamila, wannan lokaci kuwa shine lokacin da bai samu kujerar shugaban majalisar tarayya ba, wanda Yakubu Dogara ya kada shi a zaɓe.
” Duk da a lokacin Gbajabiamilla ya nuna damuwar sa, amma na kwantar masa da hankali cewa ya yi hakuri, lokacin sa na nan zuwa. Gbajabiamila mutum ne mai hankali da natsuwa sannan kuma agogo ne sarkin aiki.
A nashi jawabin Gbajabiamila ya ce ” Ka bani dama in zaɓo maka mataimakin shugaban kasa, wanda zaka amince da shi, kuma ku samu ƙyaƙƙyawar fahimta. Sai dai kuma zai yi maka wannan aiki kyauta ba sai ka biya ni.
Idan ba a manta ba, tun bayan nasarar da ya samu a zaɓen fidda gwani na ƴan takarar shugaban kasa na APC, Tinubu yake lalubem wanda zai tasaya masa takarar mataimakin shugaban kasa.
Da aka tambayeshi game da haka, Tinubu ya ce wanda ya ke so na rubuce a ƴar takarda wanda shi kaɗai ya ke da mallakin takardar.
Discussion about this post