Tsohon Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya ya bayyana yadda ‘yan siyasa su ka yaudare shi ya shiga takarar sanata na FCT Abuja, amma su ka tsiyata shi ƙarƙaf ba su zaɓe shi ba.
Okiro ya ce gaba ɗaya sun tatike dukkan kuɗaɗen da ya tara a rayuwar sa.
Mike Okiro wanda ya yi Sufeto Janar na ‘Yan Sanda daga 2007 zuwa 2009 a zamanin mulkin Umaru ‘Yar’Adua, ya bayyana wannan halin takaici da ya ke ciki, a wurin wani taron siyasa da wata ƙungiya ta shirya, wato NNDI.
Sai dai kuma babu tabbacin ko wace rana ce ya yi wannan kakkausan kalaman.
Ya ce bayan ya yi ritaya daga aikin ‘yan sanda, wani gungun ‘yan siyasa sun same shi, sun ba shi shawara cewa ya shiga siyasa. Amma bayan ya shiga, sun tatse masa kuɗi ƙarƙaf kuma sai su ka ƙi zaɓen sa.
Wannan fallasa da Okiro ya yi wa ‘yan siyasar da bai ambaci sunan su ba, ta zo ne a daidai lokacin da a faɗin Najeriya ake kuka da irin salon kuɗaɗen da masu fitowa takarar zaɓen fidda-gwani ke rabawa ga Wakilan Zaɓen ‘Yan Takara, wato ‘delegates’ na zaɓen 2023.
Okiro wanda ɗan asalin Jihar Ribas ne a Kudu maso Kudu, ya ce talakawa masu zaɓe su ne ma babbar matsala ga gwamnati.
Daga nan ya yi kira ga ‘yan Najeriya su yi watsi da karɓar cin hanci daga hannun ‘yan siyasa, matsawar su na fatan Najeriya ta ci gaba.
“Za ka ji ‘yan Najeriya na zagin shugabanni su na cewa su ne matsalar ƙasar nan. Amma ba haka ba ne. Saboda dutse ɗaya dai ba ya amo, domin masu zaɓe ne ke zaɓen baragurbi. Kuma idan mun ga shugabanni na abin da bai dace ba, talakawa dariya kaɗai su ke yi, ba su damu ba.”
Ya ce amma idan ana taka wa ‘yan siyasa burki, to ba za su riƙa yin abin da su ka ga dama ba.
“Idan aka ba ka naira 5,000 ka karɓa, to ka sani cewa waɗannan 5,000 ɗin su ne rabon ka a shekara huɗu da ɗan siyasar da ya ba ka kuɗin zai yi kan mulki. Ba zai tsinana maka komai ba.” Inji Okiro.
Discussion about this post