Saɓani ya ɓarke tsakanin Gwamnatin Jihar Sokoto da Hukumar Shirya Jarabawar Kammala Sakandare (WAEC), yayin da cacar-baki da zafafan wasiƙu su ka fara karakaina tsakanin ɓangarorin biyu.
Wakilin mu ya yi hira ta wayar tarho da bangaren jami’an gwamnati da kuma ɓangaren hukumar WAEC mai shirya jarabawar fita sakandare, wato WASSCE.
A ranar 9 Ga Mayu ne WAEC ta bayyana adadin ɗaliban da za su yi jarabawar WASSCE ta shekarar 2022.
A cikin sanarwar ta ce jihohin Sokoto da Zamfara ba su bayar da sunayen ɗalibai ko ɗaya tal ba, waɗanda za su yi jarabawar daga makarantun gwamnati.
Binciken PREMIUM TIMES ya gano cewa wasu makarantun sakandare ƙalilan ne na gwamnati, waɗanda ke ƙarƙashin Ma’aikatar Kimiyya da Fasaha ta Jiha su ka fara yi wa na su ɗaliban rajistar zaunawa rubuta jarabawar WASSCE.
Amma Ma’aikatar Ilimi ta Jiha wadda ita ce ke da ɗimbin dalibai da ya kamata a ce sun rubuta jarabawar samun shaidar kammala sakandare, domin tafiya makarantun gaba da sakandare, tun 2021 su ka daina tura sunayen ɗalibai a Hukumar WAEC, domin su rubuta jarabawa.
Yayin da Gwamantin Jihar Sokoto ta zargi WAEC da maida jarabawar wata hanyar kasuwancin tara kuɗaɗe, ita kuma WAEC ɗin ta ce ƙarya jihar Sokoto ke yi mata.
Maimakon haka, ta ce jihar Sokoto ce ta ƙi bin ƙa’idoji da sharuɗɗan da WAEC ta shimfiɗa.
Hankalin WAEC Ya Karkata Wajen Tara Kuɗaɗe, Maimakon Makomar Yara Ɗalibai -Kwamishinan Ilmin Sokoto:
Kwamishinan Ilmi na Jihar Sokoto ya zargi WAEC da maida hankali wajen tara kuɗaɗe da sunan kuɗaɗen yi wa ɗalibai rajista, maimakon bayar da fifiko wajen ganin yara ɗalibai sun samu kyakkyawar makoma nan gaba.
Guiwa ya ce an samu kurakurai sunayen ɗaliban da aka yi wa rajista a 2021. Amma maimakon WAEC ta bari a gyara kura-kuran, sai ta nemi wai sai an biya ta wasu maƙudan kuɗaɗe daban kafin ta yi gyaran.
Sai dai kuma Guiwa bai shaida wa PREMIUM TIMES adadin kuɗaɗen da WAEC ta nema a biya ta ba.
“Cikin 2021 mun samu matsalar shigar da makin auna fahimtar ɗalibai, wato ‘continuous assessment’, wanda aka loda a cikin rumbun WAEC na intanet (portal).
“An samu matsalar cakuɗa maki wajen shigarwa, sannan kuma an samu akasi an cakuɗa sunaye a bisa kuskure. Kuma ni da kai na na riƙa haƙilon tuntuɓar WAEC a kan wannan lamari.
“Amma ƙiriƙiri WAEC ta sare mana guiwa, a ƙaƙaba mana wasu kuɗaɗe da rana kata, ta ce sai mun biya.
“Ni ban yi amanna da mayar da WAEC wata hukumar tara kuɗaɗe ba. Kowa ya san hukuma ce da ya kamata ta ɗora ɗalibai kan hanyar kaiwa ga samun nasarar matakan ilmi a gaba. Amma ita WAEC a yanzu ba hakan ta ke ba.”
Guiwa ya ce Jihar Sokoto da WAEC sun yi ta antaya wa juna aiken wasiƙu a cikin 2021. Amma a haka Sokoto ta haƙura, ta ga kawai gara ta yi wa ɗaliban jihar rajistar rubuta jarabawar SSCE, wadda Hukumar Shirya Jarabawa ta Ƙasa (NECO) ke shiryawa a ƙarƙashin Hukumar NBTEB.
Guiwa ya ce NABTEB da NECO kuma duk an amince da su, domin hukumomin shirya jarabawa ne da Gwamnatin Najeriya ta kafa.
Ya ce “shin akwai wata dokar da ta ce tilas sai ɗalibi ya rubuta rubuta WASSCE sannan za a ɗauke shi makarantar gaba da sakandare ne? Ai babu.
“Kuma mu babu wanda zai yi mana wata burga ko yaudarar cewa WASSCE da WAEC ke shiryawa ta fi NECO daraja ko fa’idar fifiko. Ai dukkan ɗaliban mu su na amfani da sakamakon NECO su na wucewa gaba, ba tare da samun wani cikas ba.” Inji Guiwa.
Jihar Sokoto ‘Yar Sharri Ce -WAEC:
A martanin da ta bayar, WAEC ta ce jihar Sokoto “sharri kawai ta ke yi mata, maimakon ta fito ta tunkari matsalar gadan-gadan.”
Cikin tattaunawa da PREMIUM TIMES, HNO ya zargi Sokoto da cire ilahirin sakamakon Jarabawar Auna Fahimtar Ɗalibai (continuous assessment) da ta rigaya ta ɗora a rumbum WAEC na intanet cikin 2021. Kuma idan ana son sake ɗora wannan sakamakon, to tilas sai kowace makarantar da ke jihar an biya mata Naira 100,000.
Maimakon Sokoto ta biya kuɗaɗen, sai ta ce ita ko sisi ba za ta biya ba.
Ya ce WAEC ba ta taɓa riƙon wata makaranta ko jiha ta yi wa ɗaliban ta rajista da zauna jarabawar ta ba, kuma ba za ta taɓa yin hakan ba.
Discussion about this post