Tun bayan ficewar bayan tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso daga jami’yyar PDP babbar mai hamayya, magoya bayan Kwankwason da aka fi sani da ƴan Kwankwasiyya, su ke bayyana adawar su ga tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar kan takarar da ya ke a jam’iyyar PDP.
Da farko Ƴan Kwankwasiyyar sun zafafa adawar su ga gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal bisa zarginsa da su ke yi da marawa ɓangaren da ke jayayya da Rabi’u Musa Kwankwaso a Kano, baya kan shugabancin jam’iyyar PDP na shiyyar Arewa maso Yamma.
A cikin watan Aprilun da ya gabata ne ɓaraka ta kunno kai a reshen jamiyyar PDP na arewa maso yammacin Najeriya, inda Sanata Rabiu Kwankwaso ya zargi Aminu Tambuwal da yin katsalandan cikin al’amuran jam’iyyar a jihar Kano.
Wannan zargi da Madugun Kwankwasiyyar ya yiwa Gwamna Tambuwal ɗin ya tunzara magoya bayansa inda su ka dinga zafafa adawa tare da sukar ƙudurin Tambuwal ɗin a ya ke da shi na neman PDP din ta tsayar da shi takara, a shafukan sadarwa na zamani musamman shafin Facebook.
Sai dai rana tsaka Ƴan Kwankwasiyyar su ka sauya salon adawar su tare kausasa hamayya zuwa kan tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar tare da yin fatan rashin nasara a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar ta PDP.
Fitattun ƴan Kwankwasiyya masu amfani da shafin Facebook sun yi ta yaɗa Farfaganda da zazzafar adawa ga takarar Atiku ɗin. A ɗaya ɓangaren kuma sun nuna goyon bayansu kai tsaye ga Gwamnan Jihar Rivers Nyesom Wike.
Ana zargin Nyesom Wike, wanda ya fito neman takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar PDP, yana da wata ɓoyayyiyar yarjejeniya tsakanin sa da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, akan zai ba shi ɗaukacin daliget ɗin da su ka fito daga jihar Kano, inda za su kaɗa masa ƙuri’a a lokacin zaɓen fidda gwani na jam’iyyar.
Sai dai da alama wannan shiri bai kai ga nasara ba domin tuni Atikun ya lashe zaɓen fidda gwani na jam’iyyar PDP, inda ya zama ɗan takarar da zai fuskanci duk wanda APC za ta tsayar a babban zaɓen shekarar 2023.
Amma duk da haka ƴan Kwankwasiyyar na cigaba da adawa da nasarar Atiku Abubakar ɗin a shafukan sadarwa da rumfunan masu shayi. Abin tambayar me ya sa ƴan Kwankwasiyyar su ka so Atikun ya fadi a zaɓen fidda gwani?
Buhari Abba Rano
Discussion about this post