Wani sabon rikici ya kunno Kai a tafiyar shugabancin jam’iyyar APC, sakamakon rashin tabbacin me zai biyo baya yayin zaɓen ‘yan takarar shugaban ƙasa na fitar da gwani.
Mataimakin Shugaban APC na Shiyyar Arewa maso Yamma, Salihu Lukman, ya rubuta wa Shugaban Jam’iyya Abdullahi Adamu wasiƙa a ranar 27 Ga Mayu, inda a ciki ya ke zargin cewa an ɗage ranar tantance ‘yan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin APC ne saboda Adamu ya ce bai samu lokaci ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari ba.
Sannan kuma Lukman ya yi zargin cewa kwamitin Shirya Taron Gangamin APC wanda a wurin za’a fitar da ɗan takara, ya kasa gudanar da aikin da aka ɗora masa.
Kwamitin dai ya na ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Jam’iyya na Shiyyar Arewa, Abubakar Kyari.
Wasiƙar mai ɗauke da shafuka uku, ya rubuta ta ne kafin a ɗage ranar da APC ta shirya yin zaɓen fidda gwani na ‘yan takarar shugaban ƙasa a ranar Alhamis.
APC ta ɗage ranar taron gangamin da ta shirya a ranakun 29 da 30 Ga Mayu zuwa 6 zuwa 8 Ga Yuni, bayan Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ƙara wa jam’iyyu wa’adin ranar rufe zaɓen ‘yan takarar shugaban ƙasa zuwa ranar 9 Ga Yuni, maimakon 3 Ga Yuni.
Aƙalla akwai masu takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin APC har mutum 23.
Lukman ya yi zargin cewa APC ta bai wa waɗanda ba tololi ba ɗinka wa jam’iyyar tigar fita-kunya, alhalin ko faci ba su iya ba.
“Abin haushi ne a ce babban lamari kamar shirya taron gangamin zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa ya kasance an damƙa shirya shi a hannun ‘yan dagaji ba.”
Lukman ya ce hatta yadda ake tafiyar da jagorancin APC a Hedikwatar jam”iyyar sam ba daidai ba ne.
“Akwai matsala sosai dangane da yadda ka ke gudanar da salon mulkin ka, ta kai idan aka cimma matsaya ka na ɗaukar dogon lokaci kafin a aiwatar.
“Sannan kuma ka na ɗaukar wani hukunci ka zartas ba tare da ka shawarce mu ba. Ko kuma sai mun cimma matsaya daya, daga baya sai ka canja ra’ayi ba tare da ka sake tuntuɓar mu ba.”
Ya ce shugabannin APC sun kauce wa tsarin biyan haraji, fansho da inshora, wanda laifi ne ga dokar ma’aikata ‘yan ƙwadago ta ƙasa.
Lukman dai ba sabon-yanka-rake ba ne, kuma ba kanwar lasa ba. Ya daɗe ya na ragargazar Ƙungiyar Gwamnonin APC, duk kuwa a cewa ya riƙa caccakar ta su a lokacin ya na Darakta Janar na ƙungiyar.
Discussion about this post