Fitaccen tsohon ɗan majalisar tarayya daga jihar Kano, Abdulmumini Jibrin ya fice daga jam’iyyar APC.
A sako da ya saka a shafin sa ta tiwita kan hakan, Jibrin ya ce zai sanar da jam’iyyar da zai tsindima nan bada daɗewa ba.
” APC ta ishe ni haka nan. Na yi iya kokarina. Daga yau kuma APC sai wata rana, lokaci yayi da zan cilla gaba a siyasa ta.
Idan ba a manta ba, Jibrin na daga cikin gaggan ƴan majalisan da suka yi ruwa suka yi tsaki wajen ganin Yakubu Dogara ya ɗare kujeran shugabancin majalisa a wancan lokaci.
Sannan kuma shine babban darektan kungiyar masoya Tinubu ya zama shugaban kasa.
Jibrin ya shiga ruɗani ne tun bayan raba jiha da yayi da wasu daga cikin masu faɗa aji a jam’iyyar APCn Kano da yayi sanadiyyar rasa kujerar ta majalisa.