Masu jiragen sama sun yi barazanar cewa tsadar man jirgin sama da kuma haraji mai tarin yawa da su ke biya zai tilasta su dakatar da zirga-zirgar jirage a ƙasar nan baki ɗaya.
Wannan barazana da su ka yi ta na ƙunshe ne a cikin wata wasiƙar da su ka aika wa Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika da kuma Hukumar Kula da Zirga-zirgar Jiragen Sama ta Najeriya, a ranar Juma’a.
Wasiƙar na ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar Serina Abdulmunaf.
Ya bayyana yadda samfurin man jirgin sama mai suna JetA1 da su ke saye duk lita 1 kan 190, lokaci ɗaya ya tashi ya koma duk lita ɗaya Naira 700.
Wannan tsadar man jirgi ya haifar da tsadar gudanar da zirga-zirgar, inda lamarin ya ƙara tsada da kashi 95 bisa 100 a Najeriya
“Kamfanonin jiragen sama sun yi taro da Gwamnatin Tarayya, Majalisar, NNPC da manyan dillalan mai, amma lamarin bai canja ba.
“Mun yi taron ne domin a samu a rage tsadar farashin man jiragen sama, amma ba a yi nasara ba.” Inji shi.
Ya ce wannan tsadar mai ta tilasta masu kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama su ka maida kuɗin tikitin jirgi a Najeriya har Naira 120,000 duk mutum ɗaya.
Idan ba a manta ba, tsakiyar watan Maris sai da kungiyar masu safarar jiragen sama tayi ƙoƙarin dakatar da zirga-zirgar jiragen sama, saboda tsananin tsadar man jiragen.
A lokacin ne shugaban ƙungiyar ya ce “Man da gare mu bai wuce na zirga-zirgar kwana uku ba.”
Masu kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama a Najeriya sun bayyana cewa wadataccen man da su ke da shi a ƙasa bai wuce ya kai su yin zirga-zirga da jigilar kwanaki uku kacal ba.
Sun bayyana cewa lamarin samun mai ya taɓarɓare ne saboda tsada da ƙarancin da ya yi.
Shugaban Kamfanin Zirga-zirgar Jiragen Sama na Air Peace, kuma Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Masu Jiragen Sama na Najeriya, Allen Onyema ne ya bayyana haka a wurin zaman saurare a gaban Kwamitin Binikinen Matsalar Man Jiragen Sama na Majalisar Tarayya.
Onyema ya ce ba mamaki kamfanonin jirage su fara cajin naira 120,000 a matsayin kuɗin tikitin shiga jirgi a cikin Najeriya.
Ya ce “idan farashin tikitin jirgin sama a cikin Najeriya bai kai Naira 120,000 ba nan da kwanaki uku, to zirga-zirgar ma ba za ta yiwu ba. Kuma nan da kwanaki uku ɗin ma za mu ajiye jiragen, mu daina tashi.”
Ya yi ƙorafin cewa masu sayar masu da mai sun ƙara kuɗi, amma sun ƙi sanar da su yadda su man ke kamawa a wurin su.
Onyema ya ce matsawar masu sayar da man jirgi ba su rage farashin lita ɗaya daga naira 670 da ake sayar wa masu kamfanonin jiragen sama ba, to ya kamata hukuma ta bai wa masu kamfanin jiragen sama lasisin shigo da mai kawai.
“Mu roƙon da mu ke wa Gwamnatin Tarayya shi ne a ba mu lasisin shigo da man jiragen mu. Saboda mu a nan Najeriya, abin da wasu ƙasashen ke kashewa su yi wa jirgi uku inshora, a Najeriya jirgi ɗaya kaɗai mu ke iya yi wa inshora da kuɗaɗen. Kun ga kenan harkokin zirga-zirgar jiragen sama a ƙasar matacciya ce akwai.” Inji Onyema.