Ficewar da Rabi’u Kwankwaso ya yi daga PDP ya koma NNPP, ya sa sunan jam’iyyar ya fito a faɗin ƙasar nan. Kafin nan kuwa hatta wasu ‘yan siyasa ma ko sunan NNPP bai taɓa ji ba. Rahotanni sun nuna yadda ‘yan Kwankwasiyya ke tururuwa a faɗin Arewa su na shiga jam’iyyar, musamman a Kano, inda a ko’ina daga sunan jam’iyyar ake ji zuwa ganin fastocin ta da kuma buɗe mata rassa a lunguna da saƙo-saƙo.
NNPP, jam’iyya mai kayan marmari za ka ji ana kiran jam’iyyar ko kuma jam’iyya mai kayan daɗi.
Kwankwaso dai ya ce ya fice ne daga PDP saboda rikicin shugabanci da ya dabaibaye jam’iyyar a Kano da Arewa maso Yamma.
Tun cikin 2018 Kwankwaso ke fama da matsanancin ruɗanin shugabancin PDP a Kano. Daga cikin masu adawa da shi kuma adawar cikin gida, akwai Amini Wali, Aminu Dabo. A Arewa maso Yamma kuwa, ya sha fama da Aminu Tambuwal, Gwamnan Jihar Sokoto.
A ranar Talata ne Kwankwaso ya sayi fam na takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin NNPP. Daga cikin jam’iyyar dai babu wanda ya fito domin gwabza karon zaɓen fidda gwani da Kwankwaso.
Idan za a tuna, cikin 2015 Jonathan ya kayar da Kwankwaso a zaɓen fidda gwanin PDP. Cikin 2019 kuma Atiku ya kayar da shi a wani zaɓen fidda gwani na PDP.
Yayin da wasu ke kallon Kwankwaso a matsayin wanda ke canjin jam’iyya domin cika burin sa zama shugaban ƙasa, wasu kuma na yi masa kallon mai ci-da-zuci kawai a tsawon shekaru takwas ɗin baya zuwa har zuwa komawar sa NNPP a yanzu.
Shigar sa NNPP ke da wuya aka ƙaddamar da shi a matsayin jagoran ta, matsayin da ya kasa samu kenan a PDP da APC. Gwamna Abdullahi Ganduje na Kano ne babban ɗan adawar Kwankwaso a yanzu.
Na Kawo Ƙarfi: Bayyanar ‘Third Force’, Rundunar Siyasar Kwankwaso:
A farkon wannan shekarar ce Kwankwaso da wasu manyan ‘yan siyasa suka kafa wata ƙungiyar da suka raɗa wa suna ‘Third Force’. Sun ce sun kafa ƙungiyar ce Domin ceto ƙasar nan daga dulmiyawa cikin uƙubar da APC da PDP suka jefa ta.
“Yan Najeriya sun gaji da PDP da APC. Dalili kenan ma zaɓuka biyu da suka gabata ba a fito sosai an jefa ƙuri’a a zaɓukan shugaban ƙasa ba.”
Ana yi wa NNPP wani fukafukin National Movement da Kwankwaso suka kafa. Wasu da ke cikin tafiyar har da tsohon Ministan Wasanni na Shugaba Muhammadu Buhari, Solomon Dalung da tsohon babban aminin Buhari, wanda ya rikiɗe zuwa babban maƙiyin sa, wato Buba Galadima.
Guguwar NNPP A Arewa:
NNPP ta samu tagomashi sosai a Arewa, musamman a Kano, inda ɗan takara mai farin jini na PDP a zaɓen 2019, Abba Yusuf (Abba Gida-gida) ya bi Kwankwaso cikin jam’iyyar.
A Gombe akwai irin da Nasarawa ma NNPP ta samu tagomashi, domin Farfesa Rufai Ahmed Alƙali daga Gombe ne Shugaban NNPP na Ƙasa. Alƙali tsohon Sakataren Yaɗa Labaran PDP na Ƙasa ne.
Akwai irin su Suleiman Hunƙuyi a Kaduna, Aminu Ringim a Jigawa, Ben Kuye a Kaduna.
A Kano kusan duk jiga-jigan Kwankwasiyya sun bi Kwankwaso. A Katsina ya ja zuga da dama, ciki har da tsohon Shugaban Hukumar PTF, Muttaqa Rabe, duk da dai shi bai kai ga fitowa ya ce ya koma ɗin ba.
Matsalar da NNPP za ta samu shi ne ba ta yi ƙarfi irin su Neja da Kwara da sauran jihohin Yarabawa na Kudu maso Yamma ba.
Duk da haka ana ganin jam’iyyar za ta yi tasiri a zaɓen 2023.
Ko da ya ke dai akwai masu hasashen cewa Kwankwaso ya makara, domin ko Buhari kafin ya yi ƙarfi sosai, sai da ya yi takara ya na shan kaye tukunna.
Ko yaya Kwankwaso zai karon-batta ɗauke da kansakali mai kayan marmari a 2023, to tabbas dai ko bai yi nasara ba, sai jam’iyyar sa ta fizgi na ta kason, ko da kuwa daga bakin kura ne.