Mako daya da cire dokar tilasta saka takunkumin fuska a Najeriya mutum 48 sun kamu da cutar korona ranar Talata a kasar nan.
An gano wadannan mutane a jihohi hudu da Abuja a kasar nan.
Mutum 25 ne suka kamu da cutar a jihar Legas, mutum 11 a Rivers, Kaduna 6, Abia 1 da Abuja 5.
Zuwa yanzu mutum 255,516 ne suka kamu da cutar, mutum 3,142 sun mutu.
Sassauta dokar samun kariya daga kamuwa da cutar
Idan ba a manta ba a ranar 30 ga Maris jami’in kwamitin PSC Muktar Muhammed ya sanar cewa gwamnati za ta cigaba da sassauta dokar kiyaye daga kamuwa da cutar Korona bayan an dawo daga hutun Easter.
Muhammed ya ce kasashen duniya da dama musamman Ghana sun sanar cewa saka takunkumin fuska a cikin taron mutane ba dole bane.
Ya ce gwamnati ta sassauta dokar samun kariya daga kamuwa da cutar amma kamata ya yi mutane su rika yin taka tsan-tsan domin guje wa sake barkewar cutar.
“Daga yanzu saka takunkumin fuska a cikin taron mutane ba dole bane sannan gwamnati ta dage dokar kayyade yawan mutane a taro da sauran wuraren shakatawa da cire dokar hana walwala.
“Gwamnati za ta cire sauran dokokin idannananci gaba da samun saukin cutar.
Discussion about this post