Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta bayyana cewa mutum shida sun mutu sanadiyyar gobara da aka yi a gidan man Al-masfa Global Enterprise Nigeria LTD dake Marke a karamar hukumar Kaugama.
Kakakin rundunar Lawan Adam ya ce jami’ai sun isa gidan man a lokacin da ya ke ci da wuta da misalin karfe shida na yammacin Litinin.
Adam ya ce wata tukunyar iskar gas ce ta yi sanadiyar tashin gobarar.
“Rundunar ta kwashe mutanen da suka mutu da wadanda suka ji rauni zuwa asibitin Hadeja inda a nan wasu mutum biyu suka mutu.
Ya ce Nasiru Umar mai shekara 30, Dahawi Hakilu mai shekaru 35, Hamza Adamu mai shekaru 15, Sule Hamza mai shekaru 30 da Idris Adamu mai shekaru 25 ne suka mutu a wannan gobara.
Wani da abin ya faru a idon sa ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa ma’aikatan gidan man sun gudu a lokacin da tukunyar iskar gas din ya fashe ya kam da wuta.
Ya ce duka waɗanda suka mutu na barci ne a cikin masallaci da cikin gidan man har wutan ya kai garesu basu sani.