Zargi: Wani labari da aka wallafa a shafin facebook na zargin wai Hushpuppi, wanda aka kama da laifin zamba aka kuma kai shi Amurka ya fuskanci shari’a ya sake tafka zambar dalar Amurka dubu dari hudu daga cikin kurkukun da yake daure a Amurka.
Hushpuppi bai yi zambar dalan Amurka dubu 400 kamar yadda ake zargi ba
Ramon Olorunwa Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppi sanannen mutumi ne a Najeriya. A bara, ya yi suna sosai lokacin da ya shiga labarai bayan da jami’an hukumar FBI suka cafke shi bisa zargin shi da zambar da ya shafi satar kudade ta yin amfani da yanar gizo abin da a Najeriya ake kira “Yahoo-yahoo.”
Wadansu na mi shi kallon jarimi suna yabawa irin harkallar da ya yi wanda suke kamantawa da labarai irin na almara ba tare da yin la’akari da cewa manyan laifukan da ya kamata a yi Allah-wadai da su ne ya tabka ba. Wani mai amfani da shafin na Facebook ma cewa ya yi. “Shi mazambaci ne, amma kuma ya na da kwarewa a abin da yake yi. Mutumin na da hikima.”
Bacin haka, akwai zarge-zargen da aka yi kan Hushpuppi a shafukan soshiyal mediya wadanda ke bayar da bayanai daban-daban. A watan Maris, rahotanni da dama sun yi zargin cewa Hushpuppi ya mutu. Wani kuma ya wallafa labarin da ke cewa Hushpuppi na korafin yanayin da ya ke fiskanta a kurkuku.
Duk da cewa an karyata zarge-zargen biyu, abin da ya bayyana a fili shi ne sha’awar jin batun Hushpuppi da yadda labarin ya dauki hankalin jama’a. A yanzu haka, labarin da ke yaduwa dangane da Hushpuppin shi ne ya sake yin zamban dalan Amurka dubu 400 daga kurkukun da yak e kulle a Amurka. Duk da cewa wani mai suna “Kennyblogger” ne ya wallafa labarin, an danganta batun da hukumar FBI.
A cikin rahoton an bayyana yadda Hushpuppi ya aiwatar da zambar dalla-dalla, har da zargin cewa an ba shi komfutan da ke dauke da yanar gizo a kurkukun bisa tanadin ka’idojin kurkukun na mutunta hakkin fursunoni.
“Mahukuntan Amurka sun ce duk da cewa an takaita wa fursunoni amfani da wayoyi, da bidiyo, da yanar gizo, da komfuta, saboda ‘yancin da suke da shi na samun daman yin ma’amala da kotu cikin sirri, kamar sauran fursunonin, shi ma Hushpuppi ya sami damar yin amfani da komfutar.”
Wannan zargin ya ja hankalin mutane sama da dubu biyu. An raba shi sau da yawa kuma mutane da dama sun yi tsokaci dangane da labarin.
Wani mai amfani da shafin mai suna Izuchi Onyeika, ta yi imanin cewa labarin gaskiya ne, hasali ma a cewarsa wannan kadan ne aka ji daga cikin labarin.
“Na san wannan labarin. Ku fito fili kawai ku fada mana yadda ya yi wa gwamnatin Amurka aiki a yayin da ya ke tsare,” a cewarta.
To sai dai, Ogbuji Rhoda, wata mai amfani da shafin ta yi tambayoyi ne masu bukatar amsoshi.
“Wani kurkuku? To me ya ke yi da kudin? Ina ce an ce an dora hannu a kan ajiyar shi na banki?
Wadansu jaridun Najeriya wadanda suka hada da Vanguard, Leadership da The Independent sun dauki labarin da yi zargin wai Hushpuppi ya aikata zamban daga cikin kurkukun.
Tantancewa
DUBAWA ta fara da binciken shafukan hukumar FBI da na sashen shari’a na Amurka dangane da batun. Sakamakon da aka samu bai nuna wani abu dangane da zargin da ake yadawa ba. Bugu da kari labarin bai bayar da adireshin shafin da ya yi mafarin bayanin ba bare ma sunayen wadanda za’a iya tuntuba dangane da batun idan ana neman karin bayani.
Da ma can ba’a rubuta labarin yadda ya kamata ba domin babu bayanai masu nagarta wadanda za su bayar da hujjoji ko tabbatar da sahihancin labarin. Ashe ma an yada labarin ta hanyoyi daban-daban.
A wani rahoton da kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya rubuta dangane da wani zargin da ke kama da wannan, Thom Mrozek, darektan hulda da kafofin yada labarai a ofishin Antonin Amurka a Los Angeles ya tabbatar da rashin sahihancin labarin.
Mrozek ya ce “Wannan takardar na bogi ne,” ya kuma kara da cewa “Ofishin Antonin Amurka da ke Los Angeles wanda shi ne ya shigar da karar Mr. Abbas bai fitar da wani takarda ko labari dangane da wannan batun ba.”
Ya kuma bayar da tabbacin cewa: “Mun tuntubi FBI din da ake zargi shi ne ya rubuta takardar wanda shi ma ya tabbatar mana cewa ba gaskiya a ciki.”
Hade da haka, BBC ta yi watsi da wani labarin makamancin wanann wanda shi ma aka danganta da wannan takardar.
A Karshe
Har yanzu Hushpuppi na daure a kurkuku yana sauraren shari’a kuma bai aikata wata sabuwar zamba ba yayin da yake zaman kurkuku ba. Babu shakka wannan labarin ya samu karbuwa ne sakamakon abubuwan da suka faru a baya, don haka wanan zargi karya ne.