A ƙazamin yaƙin mamayar Ukraniya da ƙasar Rasha ke yi, lamarin da ya yi kama da labarin cikin littafin “Iliya Ɗanmaikarfi”, wanda aka bada labarin bayyanar wani ƙaƙƙarfan jarumi a Rasha, lamarin na neman maimaita kan sa a zahiri, inda yanzu haka dakarun Shugaba Vladimir Putin na Rasha su na ci gaba da ragargazar ƙasar Ukraniya.
A ranar Juma’a ce dakarun Rasha su ka ƙwace babbar tashar makamashin nukiliya na Ukraniya da ke yankin Zaporizlizhia, kuma su ka ƙwace yankin baki ɗaya.
Tashar makamashin nukiliya ta Ukraniya ita ce mafi girma a duk faɗin Turai baki ɗaya.
Shugaban Ukraniya Volodymyr Zelenskyy ya tabbatar da cewa yanzu tashar nukiliyar ta na hannun dakarun Rasha.
Sannan kuma ya yi tofin Allah-waddai ga Rasha, tare da yin iƙirarin cewa sojojin Rasha sun harba makamai a tashar.
“Rasha ta zama shaiɗaniyar ƙasar da a tarihin duniya ita ce ta fara harba makami a tashar nukiliya.” Inji Zelenskyy, tare da yin kira ga duniya cewa ya na buƙatar ɗaukin gaggawa.
Ranar Alhamis dama dakarun Rasha sun ƙwace garin Khersen mai mutum sama da 290,000, bayan sun kewaye garin ba shiga, ba fita, tsawon kwanaki uku.
Aljazeera ta ruwaito cewa sojojin na Rasha sun nausa gari mai arzikin tashoshin jiragen ruwa na Ukraniya, wato Mykollaine da ke bakin ‘Black Sea.’
Rasha na ci gaba da mamaye Ukraniya, tare da shan alwashin cewa ba za ta taɓa bari ƙasar Amurka da Turawan Yamma su ƙulla ƙawancen girke muggan makamai a Ukraniya, ƙasa mai maƙwabtaka da Rasha ba.