1 – Kanun Labarin da Ya Yaudari Jama’a Su Yi Tunanin Kan Cewa Shugaba Buhari Ya Riga Mu Gidan Gaskiya.
Wannan labarin wanda ya fita a jaridar PMNews a watan Yunin 2021 ya bulla da kanun da ke cewa: “Labari da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun harbe Buhari a jihar Edo.” Sai dai bayan da tantance labarin an gano cewa Buharin da ake magana a kai ba shugaba Buhari ba ne illa wani direba da kamfanin gini na Hartland.
2 – A’a! Ba’a Dora Hannu Kan Kadarorin Buhari Ba
Wani taken labarin wanda shi ma ya bulla a watan Yunin 2021 shi ma ya ce: “Labari da dumi-dumi: AMCON ta dauke dukiyoyin Buhari.” Wannan bayanin yaudara ce domin Buharin da ake magana a kai ba shugaban kasar Najeriya ba ne. Labarin na batun Abdzlfatai Buhari dan majalisar da ke wakiltar yankin arewacin Ogbomosho a majalisar dattawa.
3 – Babu Hujjar Da ta Nuna Cewa Buhari Ya Yi Barazanar Daure Shugabannin Kananan Hukumomi Kan Kudade
Ranar talata 22 ga watan Yunin 2021 wani mai suna Mr Joe Igbokwe, mamba a jam’iyyar APC kuma mai baiwa gwamnan jihar Legas shawara kan harkokin da suka shafi magudanan ruwa ya wallafa wani labari a shafin Facebook, inda ya yi zargin cewa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi barazanar daure shugabannin kananan hukumomin kasar a kurkukun kirikiri ko kuma hada su da hukumar EFCC idan har su ka baiwa gwamnonin jihohinsu kudaden da aka ba su. Babu wata hujjar da ta nuna sahihancin wannan zargin
4 – Aboubakar Hima Ya Damfari Najeriya Kan Kudaden Makamai a Mulkin Da Ya Gabata, Ba Gwamnatin Buhari Ba
Wani sakon da ya yi ta yawo a kafofin sada zumunta na soshiyal mediya na zargin wai ana neman wani dan asalin jamhuriyar Nijar bisa zargin shi da damfarar Najeriya dalan Amurka milliyan 400, da Nera milliyan 400 da kuma Euro Milliyan 10 wadanda aka ware dan sayen makamai. Wannan bayanin BA GASKIYA BA NE. Yayin da gaskiya ne hukumar EFCC ta bayyana Hima a matsayin wanda ta k enema bisa zargin shi da damfarar Najeriya, ba gaskiya ba ne wai ya yi hakan lokacin mulkin Buhari, kuma kudaden da aka ambata ba su kai haka ba. Ainihin kudaden Dalan Amurka milliyan 394, Euro Milliyan 9.9 da Nera Milliyan 369.
5 – Ba Buhari Ya YI Alkawarin Cewa Ba Za Shi Turai Duba Lafiyarsa Bayan Ya Zama Shugaban Kasar Najeriya Ba?
Takaitacciyar amsa? A’a. Doguwar amsa? Wani sakon Whatsapp ya sanar da cewa Buhari ba za shi duba lafiyarsa a kasashen Turai ba. Sakon ya yi zargin wai shugaba Buharin ya bayyana hakan ne lokacin wani jawabin da ya gabatar a Chatam House – Cibiyar nazarin harkokin kasa da kasa ranar 21 ga watan Fabrairun 2015 kafin a zabe shi zuwa ga mukamin na shugaban kasa. Wannan zargin ba dai-dai ba ne domin a binciken da aka yi, an gano takardar da ke kunshe da jawabin da ya yi a wancan lokacin kuma babu wani abu makamancin haka a cikin bayanan da ya yi.