‘Yan bindiga sun kashe mutum shida sannan sun saci dabbobi da dama a kauyuka biyu da suka kai wa hari a jihar Sokoto.
Maharan sun afka kauyukan Kwargaba dake karamar hukumar Wurno da Gatawa dake karamar hukumar Sabon Birni tsakanin daren Laraba zuwa yammacin Alhamis.
Jihar Sokoto kamar yadda jihohin dake Arewa maso Yammacin kasar nan na fama da hare-haren ‘yan bindiga da suka hada da kisa da sace-sacen mutane da dabobbi.
Kananan hukumomin Wurno da Sabon Birni a Gabashin Sokoto na cikin kananan hukumomin dake yawan fama da aiyukan ‘yan bindiga a jihar.
Gatawa
Wani mazaunin kauyen Basharu Altine ya ce manoma hudu ne aka kashe yayin da suke aiki a gonakin su a lokacin da maharan suka kai wannan hari.
“Mun samu labarin cewa wasu makiyaya da shannun su suke nemi manoma su siyar musu da shinkafa inda manoman suka ki. Hana su shinkafan yasa makiyayan suke musu wai sun cika son Kai sannan suka tafi. Jim kadan sai ga makiyayan sun dawo da abaokansu da bindigogi inda suka shigo gonan shigakafan suna harbin kan mai uwa da wabi.
“Garin haka aka kashe mutum hudu daga cikin manoman dake aiki a gonan shinkafan.
Altine ya ce ya san mutum daya daga cikin mutum hudu din da aka kashe domin sunan sa ‘Jirhin Laka’.
Ya ce tuni har an yi jana’izan wadannan manoma hudu din da aka kashe.
Kwargaba
Mazauna kauyen sun ce ‘yan bindigan sun afka kauyen da misalin karfe 10:25 na daren Laraba a kan babura suna harbi ta ko Ina.
Kwargaba kauye ne dake kusa da babban birnin Sokoto.
Wani mazaunin garin Mukhtar Abubakar ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa ‘yan bindigan dauki tsawon awowi hudu suna tabargaza.
“Sun shigo kauyen da misalin karfe 10:25 amma ba su suka fice ba sai karfe 1:30 na dare. Duk da cewa mun kira jami’an tsaro amma ba su suka zo ba sai da garin Allah ya waye.
“Maharan sun kashe mutum biyu, da dama sun ji rauni sannan sun saci kaya da dabbobi.
Discussion about this post