Gwamnan jihar Gombe Inuwa Yahaya ya bayyana cewa samar da kiwon lafiya da rage cinkoso a manyan asibitocin gwamnati na daga ckin dalilan da ya sa aka gyara cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a jihar.
Yayaha ya fadi haka ne a taron da ya yi da ‘Gavi, The Vaccine Alliance’ da aka yi a dakin taro dake fadan shugaban ƙasa a Abuja.
Yahaya ya bayyana cewa a cikin kwanakin nan gwamnatin sa ta rika ware kashi daya daga cikin kasafin kudin gwamnatin jihar da na kananan hukumomin domin farfado da cibiyoyin kiwon lafiya a jihar.
“Hade da kudaden da gwamnati ta ware na BHCPF da kaso daya daga cikin kasafin kudaden shekara za a yi amfani da su wajen farfado da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko ta ƙasa.
Yahaya ya ce inshoran lafiya mai taken ‘GoHealth’ ya fara aiki a jihar sannan mutum 40,000 sun yi rajista da tsarin inda a ciki akwai ‘yan gudun hijira daga jihohin da suke makwabtaka da su dake cikin tsarin.
“Inganta cibiyoyin kiwon lafiya da gwamnati ta yi ya sa an samu kwararrun ma’aikata da suke a shirye su yi aiki a asibitocin gwamnati a mai makon asibitocin dake masu zaman kansu.
“Farfado da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farkon ya taimaka wajen karfafa gwiwowin mutane wajen zuwa asibiti matuka a jihar.
Taron ya jinjina namijin kokarin da Yahaya ya yi wajen amfani da karancin kayan aiki domin inganta rayuwar mutane a jihar.
Kwamishinan lafiya na jihar Habu Dahiru, mashawarcin gwamnan kan harkokin kassafin kudi Usman Aliyu-Garry na daga cikin tawagar da suka rako gwamna zuwa wurin wannan taro.
Discussion about this post