A ranar Alhamis ne rundunar ‘yan sanda a Ede jihar Osun suka maka wani baragurbin likita Yusuf Olaniyi mai shekara 45 a kotu bayan an kama shi da laifin yanke wa wata mara lafiya hannu.
Kotun ta gurfanar da Olaniyi bisa laifin rashin iya aiki, kokarin yin kisa, karya da sana’ar likita da tada hankalin mutane.
Lauyan da ya shigar da karar Rasak Lamido ya ce Olaniyi ya aikata haka tsakanin ranar 3 ga Agusta da ranar 27 ga Nuwanbar 2021.
Lamidi ya ce Olaniyi wanda ke karya cewa shi likita ne ya yanke hannun wata mara lafiya duk da cewa ba shi da masaniya akan aikin likitanci.
Lamidi ya ce hakan da Olaniyi ya yi ya saba wa sashe 344, 484 da 249 na dokar ‘Criminal code’ na shekarar 2002 na jihar Osun.
Bayan haka Lauyan dake kare Olaniyi, T. O Shittu ya roki kotun da ta bada belin Olaniyi.
Alkalin kotun O. Ajala ya bada belin Olaniyi akan Naira 500,000 tare da gabatar da shaidu biyu a kotun.
Ajala ya ce Olaniyi zai gabatar da shaidun dake biyan gwamnatin jihar haraji sannan kuma suke zama a wurin da kotun take da Iko.
Ya kuma ce Olaniyi ya tabbatar cewa daya daga cikin shaidun ma’aikacin gwamnati ne dake mataki na 10 sannan daya dan uwan sa ne.
Ajala ya ce duka shaidun za su gabatar da hotunan fasfo dinsu da takardan shaidun biyan haraji ga rajistan kotun.
Za a ci gaba da shari’a ranar 15 ga Afrilu.
Discussion about this post