Dakataccen Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda, Abba Kyari da ke tsare, ya maka hukumar NDLEA mai tsare da shi a kotu, ya na neman ta biya shi diyyar ɓata masa suna da tsare shi ba bisa ƙa’ida da Kyari ɗin ya ce hukumar ta yi.
Waɗannan buƙatu da Kyari ya nema a kotu, suna cikin wata ƙara da lauyan sa ya shigar a Babbar Kotun Tarayya ta Abuja.
Ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/182/22, an shigar da ita ce a gaban Mai Shari’a Inyang Ekwo, har ila yau lauyan Kyari ya nemi NDLEA ta nemi gafara ga Kyari s rubuce, saboda tsare shi da ya ce an yi ba bisa ƙa’ida ba.
Ya ce ya na so NDLEA ta buga sanarwar ba shi haƙuri da neman afuwar sa saboda ba a bisa haƙƙin doka aka kama shi har aka tsare shi ba.
Lauyan Kyari mai suna C. O. Ikena ya shigar da ƙarar a ranar 17 Ga Fabrairu. Sannan kuma ya nemi kotu ta hana NDLEA ko Hukumar ‘Yan Sanda ko ma wata hukumar tsaro sake yi wa Kyari barazana, neman sa, kamshi ba bisa ƙa’ida ba.
“A matsayi na na lauyan wanda ke ƙara, ina neman kotu ta tilasta Hukumar NDLEA biyan shi wanda na ke karewa ɗin diyyar naira miliyan 500, saboda kashi da tsare shi da ta yi ba bisa tsarin da doka ta tanadar ba.
“Kamawar da aka yi masa ta keta masa ‘yancin sa na haƙƙin walwala kamar yadda Doka ta Sashe na 35 da 36 na Kudin Mulkin Najeriya ya tanadar masa.”
Lauyan ya nemi kotu ta bayyana cewa kama Kyari da tsare shi ba tare da gurfanar da shi a kotu ba zuwa ranar 12 Ga Fabrairu, ya keta masa ‘yancin sa.
Sannan kuma ya yi nuni da cewa an tozarta Kyari, an wulaƙanta shi kuma an suburbuɗe shi a inda ya ke tsare.
“Kuma hana belin sa ma wani nau’i ne na cin mutuncin sa da tauye masa ‘yancin da kundin dokokin Najeriya ya ba shi.
Abubuwan Da Suka Biyo Bayan Kama Abba Kyari:
Yadda Abba Kyari Ya Riƙa Mu’amala Da Gaggan Dillalan Hodar Ibilis Daga Brazil -NDLEA:
Hukumar Hana Tu’ammali Da Muggan Ƙwayoyi (NDLEA), ta nesanta jami’anta daga tu’ammali da hodar ibilis mai nauyin kilogiram 25 ɗin da aka kama wasu gungun ‘yan sanda da ita, bisa jagorancin dakataccen ɗan sanda Mataimakin Kwamishina Abba Kyari.
Kakakin NDLEA Femi Babafemi ya bayyana a cikin wata sanarwa a ranar Laraba cewa.
Ya ƙaryata alaƙar da ake ce ke tsakanin jami’an NDLEA na filin jirgin saman Enugu da waɗanda su ka shigo da hodar ibilis a filin jirgin daga Addis Ababa, babban birnin ƙasar Habasha.
Babafemi ya ce labarin ƙarya ce kawai wasu ‘yan sanda suka riƙa watsawa.
Babafemi ya ce bincike ya nuna cewa Abba Kyari da gungun wasu ‘yan sanda yaran sa ne ke da alaƙar kai-tsaye da wasu gaggan dillalan muggan ƙwayoyi a Brazil.
“Bincike ya tabbatar cewa Abba Kyari ne da yaran sa dillalan ƙwayoyin su ka yi mu’amala tare. Kuma binciken ya nuna yadda su ke aiki tare.”
Mugu Ba Shi Da Kama: Yadda Abba Kyari Da Yaran Sa Ke Shirya Safarar Muggan Ƙwayoyi Da Gaggan ‘Yan Ƙwayar Brazil:
“Idan za a iya tunawa bayan NDLEA ta nemi Hukumar ‘Yan Sanda ta ba su Abba Kyari da yaran sa domin su yi masu tambayoyi, ‘yan sandan sun yi masu tambayoyi sannan suka damƙa su ga NDLEA, tare da rahoton tambayoyin da suka yi masu.” Haka Babafemi ya bayyana.
Babafemi ya ce wani ɗan sanda da ke cikin gungun yaran Abba Kyari mai suna James Bawa, ya tabbatar cewa ya yi magana da wani ejan ɗin dillalin ‘yan ƙwaya da ke Brazil, kafin a shigo da sunƙin ƙwayoyi a ranar 19 Ga Janairu, 2022.
Baki Shi Ke Yanka Wuya: Mummunar Shaidar Da ‘Yan Sanda Suka Yi Wa Abba Kyari A Gaban NDLEA:
Kakakin NDLEA Babafemi ya ci gaba da cewa rahoton ‘yan sanda ya nuna: “Mataimakin Sufurtandan ‘Yan Sanda Bawa ya rubuta bayani a gaban ‘yan sandan bincike cewa wani ejan ɗin dillalan ƙwaya da ke Brazil da ake wa laƙabi da KK, ya kira shi ya sanar da shi cewa za a shigo da sunƙi-sunƙin ƙwayoyi ta filin jirgin saman Enugu.”
James Bawa ya shaida wa ‘yan sanda cewa wani da IK ya kwatanta masu shi ta waya ya samu James Bawa ɗin a ranar 19 Ga Janairu, 2022 wajen ƙarfe 2:30 na yamma, a wajen filin jirgin, inda ya nuna masa hoton sunƙin ƙwayar.
“Daga nan su ka hango wanda ake zargin a lokacin da ya ke fitowa daga filin jirgi, bayan ya gama wuce dukkan shingayen bincike. Sannan aka kama shi tare da wani abokin burmin sa.”
A cikin zancen da Abba Kyari ya yi wani jami’in NDLEA, wanda ya yi wa Kyari shigar-burtu a matsayin cewa shi ma ɗan ƙwayar ne, Kyari ya labarta masa irin yadda suka tsara shigo da hodar koken shi da ejan ɗin Brazil.
Sannan a cikin bidiyon Kyari ya bayyana yadda aka tsara yadda za a yi kason kuɗaɗen ƙwayar.
“Yayin da Abba Kyari ke amsa tambayar mu shin ko a cikin filin jirgi ko wajen filin jirgin ya ke girke yaran sa? Sai Kyari ya ce, ” ƙwarai ƙwarai, ana ajiye wasu a waje, wasu kuma a cikin filin jirgin.
“Za su bar ka sai ka gama fitowa daga ƙofar fitowa, sai su damƙe ka da ka fito waje.”
Babafemi ya ce hakan ya nuna cewa ‘yan sanda ne su Kyari su ke shirya tu’ammalin su.