A Kotun shari’a dake Rigasa a jihar Kaduna ne wata matan aure mai suna Shamsiyya Abdullahi ta bayyana cewa a shirye take ta mayar wa mijinta Ismail Bello kudin sadakin da ya biya nata naira 70,000 da akwatina biyu da ya yi na lefe.
Alkalin kotun Malam Salisu Abubakar-Tureta ya amince da haka sannan ya ce Bello zai iya rike turaman zannuwa biyar da sauran kayan dake cikin akwatin.
Tureta ya ce Bello zai rika biyan Shamsiyya naira 6,000 duk wata kudin ciyar da ‘yar su daya da suka haifa tare.
Mafi yawan lokutta mata kan hakura da aure a dalilin matsalolin da sukan fuskanta a gidajen mazajen su.
A lokaci da dama matsalar rashin nuna godiya na daga cikin dalilan da ya sa mata ke ficewa daga gidajen auren su. Sai dai kuma sau da yawa idan suka fice ɗin sai su dawo suna da na sani.
Hakuri dai shine maganin zaman duniya. Dole sai an ruka hakuri da juna ana kuma godewa juna da yin tattali a duk halin da aka faɗa ciki.
Wasu aurarrakin dole a raba su saboda zaman ba zai yiwu ba. Idan hakan ya zama dole to a rabu cikin mutunci musamman idan Allah ya azurta wannan aure da ƴaƴa.
A riƙa hakuri sannan a ji tsoron Allah.