Akalla mutum 11 ne aka kashe a kauyen Kurmin Masara dake karamar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna.
Kwamishinan tsaron jihar Samuel Aruwan ya sanar da haka a takarda da aka rabawa manema labarai ranar Litinin a garin Kaduna.
Aruwan ya ce ‘yan bindigan sun yi wa rundunar sojin sama da suka yi kokarin kawo dauki a yankin zobe.
Ya ce an samu tabbacin mutum 11 sun mutu sannan da dama sun ji rauni a jikinsu a dalilin harin.
Aruwan ya ce gwamnan jihar Nasir El-Rufa’i ya yi alhinin rasuwar wadanda aka kashe. Ya aika da sakon ta’aziyarsa ga iyalai da ‘yan uwan wadanda suka rasa rayukan su a harin sannan ya yi wa wadanda suka ji rauni addu’ar Allah ya basu lafihya.
Jihar Kaduna na daya daga cikin jihohin yankin Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya dake yawan fama da hare-haren ‘yan bindiga a kasar nan.
Sauran jihohin dake fama da wannan matsala sun hada da Katsina, Sokoto da Zamfara.
‘Yan bindiga sun ci gaba da kai wa mutane hari a wadannan jihohi duk da cewa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi alkawarin karo jami’an tsaro domin kawo karshen matsalan.
Idan ba a manta ba a cikin makon jiyab kwamishina Aruwan a madadin gwamna Nasir El-Rufai a taron mahukunta da wakilan jama’a da sarakunan gargajiya na kananan hukumomin Kauru da Zangon Kataf cewa sama da mutum 300 aka kashe a tsakanin wadannan kananan hukumomi a cikin shekarar bara zuwa yanzu.