Hukumar EFCC na tuhumar tsohon gwamnan jihar Imo, sanata Rochas Okorocha da laifin hada baki da wasu jigajigan APC da wasu kamfanoni na sace naira biliyan 2.9 kudaden jihar Imo.
Hukumar EFCC ta shigar da kara a babbar kotu a Abuja ranar Litinin da hakan ya zo kwanaki kadan da Okorocha ya bayyana aniyar sa ta fitowa takarar shugaban Kasa don maye Buhari a 2023.
Zan yi takarar shugaban kasa
Tsohon gwamnan jihar Imo sanata Rochas Okorocha ya bayyana niyyarsa na fitowa takarar shugabancin Najeriya.
Okorocha ya ce zai gudanar da taron ‘yan jarida na duniya wanda za a yi 31 ga Janairu a Abuja.
A takardar wanda aka raba wa manema labarai ranar Laraba a Abuja Okorocha ya ce zai fito takarar shugabancin Najeriya a 2023 ne domin ya fidda Najeriya daga matsalolin da take ciki.
” Zan yi taron ‘yan jarida ranar 31 ga wata. A wannan rana zan bayyana wa duniya niyya ta da irin abinda nake da burin yi wa kasa ta Najeriya idan na zama shugaban kasa.
Okorocha ya shiga cikin jerin wasu manyan yan siyasan Najeriya da suka bayyana niyyar su na yin takarar shugaban kasa a 2023.
Wadanda suka suka bayyana ra’ayin su sun hada da tsohon gwamnan Legas Bola Tinubu, tsohon mataimakin babban bankin Najeriya, Kingsley Moghalu, Mawallafi Ovation, Dele Momodu, gwamnan jihar Ebonyi David Umahi, tsohon shugaban majalisar dattawa Pius Anyim, Sam Ohuabunwa da Khadijat Okunnu-Lamidi.
Discussion about this post