Hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko ta jihar Bauchi, BSPHCDA ta bai wa mutum 987,635 maganin cututtukan da mazauna karkara suka fi fama da su wato ‘Neglected Tropical Diseases (NTD)’ a shekarar 2021.
Jami’in hukumar BSPHCDA Sanusi Ishaku ya ce an bai wa wadannan mutane magunguna a kananan hukumomi biyar da suka hada da Kirfi, Bogoro, Warji, Giade da Toro.
Ishaku ya fadi haka bayan an tashi taron wayar da kan mutane game da cututtukan NTDs na shekarar 2022 da aka yi a karamar hukumar Toro ranar Juma’a.
Ya ce baya ga bada magani hukumar ta yi wa wadanda cututtukan su ya kai ga a yi musu aiki fida sannan cututtuka irin su Onchocerciasis, ciwon dundumi, tsutsan ciki da ciwon Ido na daga cikin cututtukan da mazauna kananan hukumomin suka fi fama da su.
Ishaku ya ce duk shekara a lokacin bazara hukumar kan shiga kauyuka domin bai wa mutanen dake fama da irin wadannan cututtuka magani musamman a kauyukan dake da wahalar zuwa.
Bayan haka shugaban hukumar Dr Rilwanu Mohammed ya ce a bana BSPHCDA ta zabi kananan hukumomi 19 daga cikin 20 din dake jihar domin kula da duk mutanen dake fama da irin wadannan cututtuka.
Mohammed ya kuma ce hukumar za ta zuba magungunan warkar da sarar macizai da cizon kare domin fadada kulan da mutane za su rika samu.
Shugaban fannin kula da masu cututtukan NTDs na shiyar Arewa maso Gabas na ma’aikatar kiwon lafiya Hauwa Abubakar ta ce cututtuka irin su NTDs cututtuka ne da ake warkewa.
Hauwa ta ce rashin samun tsaftataccen ruwa, rashin tsaftace muhalli na daga cikin dalilan dake yada wadannan cututtuka.
Kodinatan BSPHCDA na jihar Nasiru Baba ya ce shirin bai wa masu fama da cututtukan NTDs da hukumar BSPHCDA ke yi duk shekara na samun goyan bayan Kungiya mai zaman kanta MITOSATH.
Baba ya yi kira ga duk masu fama da irin wadannan cututtuka da su fito su karbi maganin a duk lokacin da hukumar ke badawa kyauta.
Discussion about this post