Jam’iyyar PDP a jihar Kaduna na gab da faɗawa cikin mummunar ruɗanin da idan bata yi da gaske ba zai iya sa APC ta samu raɓas, garas, wato gasassa daga sama a zaɓen gwamnan jihar a 2023.
Ga dukkan alamu duka waɗannan jigajigan PDP ɗin sun fallo takubban su kowa ya jawo banten sa zai ɗaura ɗamarar fafatawa a zaɓen fidda gwani tukunna kafin a tunkari zaɓen kifa ɗaya kwala wato, mai gaba daya a watan Faburairun 2023.
A baya dai Honarabul Isah Ashiru ke kan gaba wajen neman cira tutar jam’iyyar PDP a zaɓen gwamna, sai dai kuma tsindimar sanata Shehu Sani jam’iyyar PDP da kuma bayyana ra’ayinsa na fitowa takarar gwamna Kaduna a Jam’iyyar PDP ya na neman ya dagula wa ƴan takarar jam’iyyar lissafi. Sannan kuma ga tsohon gwamna Ramalan Yero shima ya ce wannan karon sai yaga abin da ya ture wa buzu nadi.
Akwai kuma jigon jam’iyyar wanda aka fisani da ‘yanka ɗaya’ wato Sule Hunkuyi wanda shima jigo ne a siyasar PDP bai ce komai ba tukunna.
Abin lura a nan shine anya a cikin waɗannan Ƴan takara akwai wanda zai iya janye wa wani kuwa a wannan karo musamman ganin ba Nasir El-Rufai bane zai yi takarar gwamna sai wanda ya zaba wato ɗan lelen sa.
Hakan ya sa kowa na ganin idan aka buga lissafi mai kyau akwai alamun PDP za ta yi tasiri fiye da yadda ta yi a baya a jihar, domin kuwa ɗan takara shine zai sai da kan sa.
Sai dai kuma zaɓi ya rage wa mutanen jihar Kaduna domin wasu na ganin dukkan su ba za su iya kada ɗan takaran APC ba wanda El-Rufai zai tsayar dubi da irin ci gaban da aka samu a jihar Kaduna babu kakkautawa tun bayan ɗarewar gwamnatin APC a 2015.
A wani ɓangaren kuma babban abin tambaya da yin nazari a akai shine, shin mutan Kaduna suna so su koma ga mulkin PDP ko kuma suna ganin salon mulkin El-Rufai da wanda zai tsayar musu yafi musu akan wadannan jerin ƴan takara na PDP.