Dattijo Sa’idu Dabo ya gamu da tsautsayin yin garkuwa da shi a gonar sa a garin Faskari inda yan bindiga suka yi awon gaba da shi suka kuma tsare shi har kwanaki 11 kafin suka sake bayan an biya su naira 50,000.
Sai dai kuma tsautsayin bai tsaya nan ba domin bayan dan sa Ibrahim ya kawo musu wannan kudi sai kuma suka yi garkuwa da shi suka umarci mahaifin nasa Dattijo Sa’idu ya koma gida ya kawo musu naira 100,000.
A dalilin haka ne ya sa mahaifin Ibrahim ya cire rufin kwanan gidan sa ya saida ya aika wa ‘yan bindiga.
Kalli bidiyo:
[youtube https://www.youtube.com/watch?v=y5mpG3Gjhks&w=760&h=365]