Shin kuwa muna nazarin yanayin da Arewacin Nijeriya ta samu kanta na tashin hankali da kasha-kashe da ya addabi wannan yankin na Nijeriya? Shin ya ya muke hangen goben Arewacin Nijeriya?
Musamman wajen nazarin shekarun mutanen da ake zargi wajen aikata wadannan taáddancin irn na satar mutane don neman kudin fansa, fashin daji da bindiga-dadi.
In muka yi duba na tsanaki, zamu ga shekarun wadannan mutane mafi yawa daga cikin su, musamman irin wadan da jamián tsaro suke gabatarwa, za kaga akasarin su shekarun su yana tsakanin 16 ne zuwa 27, wasu ma shekarun su bai kai haka ba, wa yanda ma suka haura shekaru 30 basu da yawa a ciki, kuma duk wannan rigingimu ya yi yawa ne a Arewacin Nijeriya, kuma kullun irin wannan rikici karuwa ya keyi da chanja salo.
Idan muka yi duba da shekaru dawowar dimokaradiyya a Nijeriya na sama da shekaru 20 kusan wadannan mutanen sun girma ne a ciikin wadannan shekarun. Sabo da haka akwai alamun tambaya ta yadda a ka tafikadda da tsare tsare da gudanar war alúmma musamman yara kanana, ta yadda tunanin su ya chanza zuwa wannan mummunar taádda.
Tabbas a kwai tasgaro wajen samar da dokokin da za su inganta rayuwar yara, kokarin da aka yi wajen yakar talauchi musamman a tsakanin yara kanana, kyakkyawar tsarin ilimi da kuma babbar matsala yawo da gararanbar yara, musamman a manyan biranen mu na Arewa da sunan almajiranta da yawon bara.
Wannan annoba ta gararanbar yara kullum karuwa take kamar gobarar daji. Babban abi damuwar shine bamu san yadda rayuwar wannan yaran zata kasan ce a gaba ba. Amma fa da wuyar gaske tayi kyawu.
Tsananin talauci da ya addabi yankin Arewacin Nijeriya, musamman rashin samun damar yara a wannan yankin na samu ingantacciyar rayuwa da za ta basu damar samun rayuwa irin wanda a ke tsanmani ga kowa don samun kyakkyawan zaton cika burin rayuwa mai kyawu kamar kowane dan adam, musamman samun ilimi na zamani, samun abincin mai gina jiki ga yaran don samun kyakkyawan tunani da zai samar da ilimin da ake bukata don gina rayuwar da za ta taimaki alúmmah da kasa baki daya.
A wannan satin da yake karewa ne, a ranar 24 ga watan daya na wannan shekarar aka yi ranar ilimi ta duniya, abin takaici ne a jerin jahohi goma sha daya da suka yi fice wajen ci gaban ilimi a Nijeriya babu jahar Arewa ko daya kuma abin mamakin duka jahohin da ke koma baya wajen ingancin ilimi a Nijeriya duka jahohin Arewa ne. Wanda kiddiga ta nuna a wannan yankin ne yaran su basa zuwa makaranta, sune jahohin da basu da kwararen malamai a makarantun su, sune koma baya wajen ilimin ýaýa mata, sune wanda yaran su basu ciki tsayawa don kammala karatun su ba da matsaloli masu yawa da suka kawo wa tsarin bayar da ilimin kananan makaratun wannan yankin tarnaki.
Almajirancin da gararan bar yara a garuruwan mu na arewa manuniya ce ta hatsarin da wannan yankin zai shiga a nan gaba, duba da halin da ake ciki a yau.
Anjima ana maganar wannan matsala, amma maganar ba ta wuce tattaunawa ba, har yanzu babu wani babban mataki da aka ga gwamnonin wannan jahohi sun dauka kuma an basu muhimmancin don kawo karshen wannan matsalar.
Duk da kasancewar wasu da ga cikin jahohin wannan yankin a shekara ta 2020 sun yi kame da mayar da irin wadannan yaran jahohin su don maida su da iyayen su da kuma kafa dokar hana barar a kan titunan biranen su, amma anga wannan mataki bai kai ko ina ba, kai a wasu biranen ma kamar ba ayi hakan ba.
An yi harsashen cewa sama da yara miliyan biyu ne suke gararamba a jahar kano kadai da sunan bara da almajiranci.Koda a gwmantin baya an bijiro da tsarin Almajiri school ta yadda za zamanantar da wannan mummunan aláda ta yawon bara, wajen gwama karatun zamani da na arabiyya ga yara almajiran, wanda wannan shiri zai tallafi jahohin Arewacin Nijeriya ne, inda gwamnonin Arewan sun maida hankali a kansa da watakila abun bai haka yake ba a yanzu.
Duk da cewa, kamar a Jihar Jigawa a wannan gwamnatin sun kashe miliyoyin kudade don gina ajujuwa a wurare daban-daban a fadin jahar da sunan tsangaya school don ilimantar da ireren wannan yaran, amma fa ginin ne, babu wani tartibi tsari da dokar da zai zaunar da yaran nan waje guda, ta yadda za su sami ilimi da kykkyawar tarbiya.
Yau a jahohin Arewa ba ma maganar iren wadan nan yaran ba, hatta makarantun boko na zamani basu da kykkyawar kula a wajen shugabannnin mu, akasa rin kananan makarantu irin su primary, secondary schools na fama da matsaloli daban-daban kama daga rashin isassun malamai, kayan koyo da koyarwa da ma ingancin koyarwar.
Rahotannin da BBC Hausa ta bada a wannan makon ta yadda a ka samu gidan da yara ke biyan kudi domin su sami wurin kwana, bayanan da wadannan yaran suka yi abin takaici ne, kuma karara yana nuna har yanzu mutanen akwai sauran rina a kaba wajen kare hakokin wannan yara da ga shugabannin mu, wanda ya hada da samarwa da kuma aiwatar war dokar da za ta tabbatar da hakkin yaran mu, ta ganin sun sami damar zuwa makaranta kamar kowane yara a fadin duniya. Samar da dokar da za ta tilastawa iyaye kula da yaran da suka haifa.
Duk da kasancewar akwai doka a wasu jahohin na dole a san ya yara a makaranta, kiyasi ya nuna sama da yara miliyan ashirn (20 millions) da basa zuwa makaranta a Nijeriya, dukka akasarin su suna yankin Arewacin Nijeriya ne, in muka duba ta wani gefen hatta a yau samarin da suka dauki bindiga, da yan fashin daji da masu garkuwa da mutane, da wayan da suka shiga kungiyoyin irin su Boko Haram da makaman tansu, duk sun futo ne da ga wannan yankin na Nijeriya.
Wannan zai iya nuna mana makomar alúmar mu a nan gaba, in har muka sake bari rayuwar wannan yara ta samu tangarda, zai yi wahala kwarai su sami kyakkyawan tunani da makomar da zasu samawa kansu na samun aikin yi ko sanaár yi don dogaro da kai da gina kasa. Kuma a yayin da suka sami nutsuwa ba za su yafe wa shugaban nin wannan zamani ba. Domin su ba haka suka tafiyar da rayuwar nasu yayan ba.
Ya zama dole gwamnonin Arewacin Nijeriya da ma duk masu fada aji,su sake dubban wannan matsala ta ilimi da ma rayuwar kananan yara a wannan yankin, wajen yin doka da kuma tabbatar da aiwatar da ita da zai sanya tilastawa iyaye sanya yaran su a makaranta , dokar da za ta hana yawan bara a duk fadin yankin, dokar da za ta sanya ido wajen aure da kare iyali.
Allah ya kyauta.
alhajilallah@gmail.com
Discussion about this post