Kungiyar kabilar Kibaku dake Chibok ta bayyana cewa har yanzu akwai ɗaliban makarantar Chibok da Boko Haram suka sace 110 da ba a san inda suka ba.
Idan ba a manta ba Boko Haram ƙarƙashin Abubakar Sheƙau sun sace ɗalibai mata a garin Chibok a cikin watan Afrilun 2014.
Shugaban kungiyar Dauda Iliya a madadin mazauna garin Chibok ya bayyana haka a karshe makon jiya a taro da yayi da manema labarai a Abuja.
Iliya ya ce daga cikin ‘yan mata 276 din da aka sace 57 sun gudu daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su.
Ya ce har yanzu Chibok na fuskantar barazanar ‘ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane.
“A yanzu haka gwamnati ta rabu da mutanen Chibok su kare kansu daga barazanar rashin zaman tsaro da fargabar za a iya afka musu a ko da yaushe da take fama da su.
Abin takaicin dake faruwa a Chibok
Iliya ya ce tun daga shekarar 2012 zuwa yanzu Chibok ke fama da hare-haren mahara wanda suka haɗa da asarar rayuka da dukiyoyi.
Ya ce an kashe mutum sama da 72, an yi garkuwa da mutum sama da 407 , an kona gidaje, wurin kasuwanci, rumbunan hatsi da coci-coci da dama sannan an sace ababen hawa sama da 20 duk a Chibok.
Iliya ya ce tun daga karshen shekarar 2018 zuwa yanzu matsalar rashin tsaro a Chibok tsanananta.
“An Kai wa Kautikari hari a ranar 14 ga Janairu 2022 sannan yi garkuwa da mata biyar, an kashe mutum uku, an Kona gidaje da Coci da dama a kauyen.
“A ranar 20 ga Janairu mahara sun afka kauyen Piyemi inda suka yi garkuwa da mutane 19 da mafi yawan su mata ne sannan suka yi wa wani ɗan kungiyar sa kai yankan rago.
“Muna kira ga gwamnati da ta bude sansanin ‘yan gudun hijira a Chibok ta kuma bude wurin horas da matasa sana’o’in hannu domin kawar da yunwa da fatara da ya addabi mutanen garin.
“Muna yi wa rundunar sojin Najeriya ta’aziyar dakarun ta da ta rasa musamman brigediya-jana B. K. Zirkushu.
Iliya ya yi kira ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da ya taimaka wajen dawo da sauran ‘yan matan Chibok gida.
A karshe ya roki manema labarai su yaɗa waɗannan bukatu nasu duk duniya kowa ya sani domin jama’ar yankin su samu saukin rayuwa.
Discussion about this post