Fitacciya jarumar fina-finan Hausa Rahama Sadau ta gargadi gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da su shiga taitayin su kada fa kwanto kura, yan Najeriya su fusata.
Sadau ta bayyana haka ne a sakon da ta wallafa a shafinta ta Instagram inda tace rayukan ‘yan Najeriya ba a bakin komai ya ke ba yanzu kama ga yadda yan bindiga suka mamaye ko ina a yankin Arewa suna kisa yadda suka dama kuma babu abinda ka aiya yi a kai.
A wannan sako wanda ta rubuta a cikin harshen turanci duk da ta saka wasu cikin harshen Hausa, Sadau ta ce Tura fa ta kai bango yanzu.
” Irin hotunan da muke gani ana saka wa a shafukan yanar gizo hutunan ne masu tada hankali matuka. Abin tambaya menene talakawan najeriya suka yi da aka bari wadannan mutane na gallaza musu azaba.
” Wai shin laifin mu shine kawai don mun Zabe su. Ina nufin dukkan su da ke kan mulki a kasar nan. Wai yaushe za a sauraremu a kawo mana dauki, a maida hankali wajen kawo karshen kisan gillar da ake yi wa mutane musamman ‘yan Arewa a yanzu. Idan kuka ji sun garzayo sun waiwaye mu to shekarar zabe ya kunnu kai ne.
” Wannan rashin tsaro yana gidan kowa a yankin Arewa, adai yi hattara kada allura ta hako garma. Talaka a yau, zama a cikin gidansa ma tsoro yake bashi.
“Idan kowa ya mutu Sai muga wanda zai zabe su. Zubar da jinin ya isa haka