Idan ba a manta ba PREMIUMTIMES HAUSA ta buga labarin yadda ‘yan bindiga suka yi garkuwa da wasu mutane 4 a kauyen Tegina dake karamar hukumar Rafi a kwanakin baya.
Daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su a lokacin akwai Jami’in kiwon lafiya Sani Garba, manajan gidan ruwa, Kasimu Lawan da wani lebura a gidan ruwan mai suna Mas’udu Ibrahim.
A lokacin ‘yan bindigan sun bukaci a biya su Naira miliyan 150 kafin a sake su.
A ranar Talata wani mamaban kungiyar motocin haya dake karamar hukumar Tegina, Bello Muhammad ya ce ‘yan bindigan sun kashe Sani Garba da Kasimu lawan bayan sun karbi Naira miliyan 8.
“Mazauna kauyen ne suka yi karo-karo suka hada Naira miliyan 8 din da aka biya kudin wadannan ma’aikata amma duk da haka suka kashe su.
Ya ce yanzu ‘yan bindigan sun ce a biya su Naira miliyan 20, babura uku da wayar salula biyu kafin su saki sauran mutanen dake hannun su.
“Mun samu labarin cewa Mas’udu Ibrahim ya gudu sai dai kuma wani Bako BK na nan tsare a hannun ‘yan bindiga.
Discussion about this post