A kotun majistare dake Ikeja jihar Legas ta bada belin wani direban babban mota mai suna Ahmed Ismaila mai shekara 28 da laifin sata da siyar da tayoyin tirela har guda 17.
Kotun ta gurfanar da Isma’ila bisa laifin hada baki da sata.
Dan sandan da ya shigar da karar sajen Olasunkanmi Adejumola ya ce Ismai’la ya aikata wannan laifi ne ranar 22 ga Oktoba a Apapa-Oshodi.
Adejumola ya ce Ismai’la ya saci wadannan tayoyi daga wajen wanda yake masa aiki Olugbenga Otolola.
Ya ce farashin tayoyin ya sun kai Naira miliyan 1.9.
“Ismai’la ya siyar da tayoyin guda 17 sya rika kashe kudin har suka kare.
John ya ce zuwa yanzu Otolola ya samu nasaran karban taya daya daga wajen wanda Ismai’la ya siyar wa.
Alkalin kotun O.A Odubajo ta bada belin Ismai’la akan Naira 200,000 sannan kuma zai gabatar da shaidu biyu dake aiki kuma suna biyan haraji wa gwamnatin jihar Legas na tsawon shekara biyu.
Za a ci gaba da shari’a ranar 25 ga Janairu 2022.