Alkalin kotun bai bayar da umurnin a yi gaggawar rufe Kotun Daurin Aure na Taryyar da ke Ikoyi, jihar Legas.
Sashen babban kotun tarayya da ke Legas ba ta bayyana aurarrakin da aka daura a kotun da ke Ikoyi haramtattu ba a cewar rahoton PREMIUM TIMES.
A hukuncin da ya yanke ranar 8 ga watan Disemba, wanda jaridar PREMIUM TIMES ta samu, mai shari’a Justis D.E Osiagor ya bayar da umurnin da ta hana ma’aikattar cikin gida daura aure a karkashin dokar aure ta kasa “sai dai idan an daura a kotun daurin auren da ke Ikoyi, Legas, da wanda ke birnin tarayya Abuja.”
Sai dai mai shari’ar bai amince da wadanda ke neman ganin ma’aikatar cikin gidan ta maido takardun auren da ta riga ta bayar da ma kudaden da ta karba daga wadanda ta daurawa auren.
Zargin
Wadansu kafafen yada labarai sun yada rahotannin cewa babban kotun tarayya a Legas ya hana gwamnatin tarayya daura aure. Rahotannin sun ce ya bayyana duk wani auren da aka daura a sashen aure na kotun Ikoyi a Legas.
A cewar jaridar ThisDay, “Kotu ta bayar da umurnin rufe duk wuraren auren da ma’aikatar cikin gida ta bude, a ciki har da wanda ke ikoyi cikin gaggawa.”
Rahotannin sun janyo cece-kuce sosai a kafofin sadarwa na soshiyal mediya, har ma yawancin masu tsokaci dangane da batun suka mayar da shi abin wasa.
Misali, a shafin tiwita Bruce Bateman Esq ya ce: Wannan ya na da alfanu. Idan har ka daura aure a kotun Ikoyi kuma kana tunanin saki ba sai ka kasha kudi ba. Ku rabu kawai da ma can auren ba ta dauru ba
#OurFavOlineDoc kuma cewa ya yi: Idan kun yi aure a Ikoyi kuma auren ya gundure ku, kuna iya rabuwa yanzu. Babu bukatar saki a hukumance.
Babu rabon kudi. Babu kudin lauyoyi. Kawai ku kira motar haya ta Uber ku kama gabanku.
Wata babbar kotu tarayya ta ce duk aurarrakin da aka daura a kotun Ikoyi bas u halatta ba.
Sai a hanzarta kafin wa’adin ta wuce.
Shari’ar
A shekarar 2018 kananan hukumomi hudu a Najeriya suka shigar da kara zuwa babban kotun tarayya da ke Legas dangane ma’aikatar cikin gida, Antoni Janar na kasa da kamfanin Anchor Dataware Solutions Limited.
Kananan hukumomin hudu sun hada da karamar hukumar Eti Osa da ke jihar Legas, Karamar hukumar Egor da ke jihar Edo, karamar hukumar Owerri da ke jihar Imo da karamar hukumar Port Harcourt da ke jihar Rivers.
A cewar masu karar, biyo bayan hukuncin da mai shari’a Justice Oyindamola Olomojobi ya yanke a shekarar 2004, kotu ta hana ma’aikatar cikin gida da wakilanta daura aure da rajistan shi da ma bayar da shaidar aure ko kuma certificate a tuance.
Masu karar na jayayyar cewa ita ma’aikatar cikin gida da mukarrabanta dokar auren ko kuma Marriage Act ta tanadi su bayar da lasisin amincewa da aure tsakanin wadanda ke shirin auren ba wai su su daura mu su auren ba.
Haka nan kuma sun bukaci kotun da ta umurci ma’aikatar ta maido da duk certificate na shaidan auren da ta bayar a kananan hukumominsu tun bayan shari’ar da aka yi a 2004.
Bugu da kari su mayar da duk wani kudin da suk karba tun wancan lokacin saboda a sake bayar da takardar shaidan ga wadanda ta yi ma auren, kafin shari’ar ta 2004 tunda yanzu kotu ta ce ba su halatta ba.
Sa’annan bukatarsu ta karshe ita a haramta wa ma’aikatar daurin auren a kuma rufe duk ofisohin da ta bude dan yin auren a jaddada mata cewa ta daina kure iyakarta tana daurin aure, ta tabbatar cewa aikinta bai wuce bayar da lasisin aure da kuma gina wuraren ibada ba.
Hukunci
A hukuncin sa, mai shari’a Mr Osiahor ya yi la’akari da cewa an yi watsu da karar da masu karar su ka shigar gaban justis Chuka Obiazor a 2017 sakamakon rashin hurumi.
A wancan karar, Mr Obiozor ya bayyana halatattun cibiyoyi da mahukuntan da ke da ikon daura aure wadanda suka hada da : rajistrori a wuraren da ke zaman ofishi; wadanda aka san su a matsayin malaman addini a wurin da ke da nagartaceen lasisi na kasancewa wurin ibada; an yi auren a karkashin lasisin da darekta janar na ma’aikatar cikin gida ya amince da shi, darekta janar na gwamnatin jihar da ke da alhakin aurarraki, ko wani ma’aikaci a daya daga cikin ofisoshin sa aka riga aka bayaana da kuma ministan cikin gida.
Mr Osiagor ya danganta shari’ar da ke gaban shi da yarjejeniyar hadin gwiwa ta gwanati da na ‘yan kasuwa/kamfani masu zaman kansun da ke tsaknain ma’aikatar cikin gidan da kamfanin Anchor Dataware Solutions Ltd inda burinsu shi ne samar da ofisoshin daurin aure a kasar baki daya.
“Da wannan yarjejeniya, ma’aikatar cikin gida ta haramta duk wani auren da aka yi a ofisoshin auren da ke kananan hukumomi ke nan,” a cewar mai shari’ar
Ya kuma kara da cewa a bisa la’akari da abubuwna da suka wajaba a kan bangarorin biyu, ma’aikatar cikin gidan ta umurci Immaigration ta mayar da shaidar aure na tarayya daya daga cikin mahimman abubuwan da ake bukata wajen neman takardar tafiya ko kuma passpo daga duk ma’aurata.
Ma’aikatar ta shawarci ofisoshin auren da ke kananan hukumomi da su nemi amincewar ofisoshin aure na tarayya saboda su ma su cigaba da aiwatar da aurarrakin kamar yadda dokar auren ta tanada.
“Ma’aikatar cikin gida da abokan hadin gwiwarsu wato kamfanonin masu zaman kan su, suna suayawa ne daga hukuma mai sanya ido zuwa wadda ke bayar da fifko ga samun kudaden shiga ta samar da ofisoshin daurin aure na daban a duk fadin kasar har da kananan hukumomin da ke da hurumin daurin auren bisa tanadin doka,” a cewar mai shari’ar
“Daukan wasu karin matakai na zuwa ofishin Immaigiration na kasa da ofisoshin jakadanci Najeriya su ce sai an bayar da takardar shaidar aure na tarayya ba wani abu ba ne illa amfani da karfin ikon gwamnati su ci zarafin mutane, wanda ya sabawa tanadin gwamnati na mutunta rassa ukun da ke shugabanci a gwamnatin Najeriya.
“Wannan abin Allah wadai ne kuma na yi tir da shi.”
Alkalin yace yunkurin ma’aikatar cikin gidan na mayar da abubuwan da suka shafi daurin auren a tsakiya ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar na 1999, ya sabawa hukuncin da justis Olomojobi ya yanke kuma wannan babban cin mutunci ne ga rassa ukun da ke zaman shugabanin gwamnatin tarayyar kasar.
“manakisan da suka kulla wajen yin gaban kansu su gindaya sabbin wuraren daurin aure a maimakon wuraren da aka riga aka amince da su ya raunana ikon kananan hukumomi bai halata ba. Babu ma’aikatar da ya kamata ta yi haka.
Alkalin y ace duk wani wurin auren da ma’aikatar ta samar wanda ya kasance a wajen tsohon babban birnin Najeriya Legas ko kuma sabuwar babban birnin wato Abuja “aikin banza ne”
Dan haka mai shari’an ya hana ma’aikatar cikin gidan da mukarrabanta “daura aure a karkashin dokar aure ta kasa a kananan hukumomin masu karar sai idan an daura a Legas ko Abuja.”
Sai dai mai shari’an bai amince da bukatar masu karar na mayar da kudi da shaidar auren da aka bayar ba.
Discussion about this post