Zargi: Wai kona takardar da aka jika a zuma na da lahani ga irin dabbobin da ke rarrafe kuma yana iya korar macizai daga gidaje ko muhallin da suka boye
Bayan mutuwar wata ma’aikaciya a ofishin dakarun sojin saman Najeriya sakamakon sarar maciji a bayin gidanta da ke Abuja, rahotannin macizai a bayi sun karu sosai a shafukan intanet, abin da ya sanya tsoro a zukatan ‘yan Najeriya har ya yi sanadiyyar bullowar shawarwari daban-daban dangane da yadda jama’a za su kare kansu daga macizai, su kuma kore su daga gidajensu da muahallin su.
Daya daga cikin irin wadannan sakonnin ya ce idan har aka kona takardun da aka jika a cikin zuma, zai kori macizai daga gidaje da ofisoshi domin hayakin na korar sa.
“ Ku kona takardar da aka tsuma a zuma a tsakar gida/ko ofishi. Bar kofofi a bude dan macizan su fita domin warin zuman na da karfi kuma ya na tayar mu su da hankali tare da hadarin gaske,” a cewar rubutun.
Hoton da aka sanya bayanin tare da hoton maciji ya shawarci mutane da su raba da ‘yan uwa da abokai domin a fadakar da mutane.
Da muka cigaba da bincike a shafin Facebook, nan ma mun ga labarin a shafin wani mai suna Sure Truth wanda shi ma ya ke tabbatarwa jama’a da tasirin kona takardar wajen korar maciji.
Labarin da Sure Truth ya rubuta a shafin shi da ke ikirarin cewa yana bayar da “nagartattun bayanai dangane da yadda ake kula da lafiyan jiki, da rayuwan iyali da ma mafi mahimmanci ganyayyaki na gargajiya irin wadanda ake shukawa a gida wadanda ke maganin cututtukan da ba sai an sha mu su na asibiti ba,” ya sa mu an raba shi har zuwa 1,700 kuma mutane sama da 500 sun nuna amincewarsu da labarin a yayin da wasu 190 su a yi tsokaci.
Wannan zargin ya sake bayyana a shafin Boboye Oyeyemi, PhD babban darektan Hukumar Kiyaye Haddurukan kan Hanya na Tarayya wato Road Safety (FRSC)
Tantancewa
Binciken da Dubawa ta yi ya nuna mata cewa kona takardar da aka jika da zuma hanya ce kawai na gane ko zumar mai kyau ne, bayan haka babu wata hujjar da ta nuna cewa kona takardar da aka jika da zuma na kora macizai.
Doug Sofranko kwararre kan dabbobi masu rarrafe ko tafiye da cikinsu, wato herpetologist a turance, ya ce babu shakka da ma akwai abubuwan da ake zargi wai suna koran macizai kamar zancen kona takardar da aka jika a zuma, alhali kuma ba ya mu su komai.
“Kona zuma ba ya aiki, haka ma kafur duk ba su aiki. Sinadaran da ke cikin kafur na da lahani sosai ga dabbobi da kwari amma bai ma maciji komai. Ban san me ya sa mutane suke ganin kamar yana aiki ba – ba ya yi,” ya ce.
Sofranko y ace macizai ba kaman ‘yan adam ba ne ba su iya jin wari dan haka ba za su iya yin amfani da hancinsu su san wai akwai hadari a gabansu ba.
“Macizai ba su jin wari ko kanshi kamar mu. Dan haka hancinsu ba zai iya sanar da su cewa akwai wani hadari dake tafe ba. Ba su iya gane wari ko kamshi kamar mutane da sauran dabbobi,” ya ce.
Maciji na amfani da harshen shi ne ya lashi kasa ko iska dan jin wari. Idan har harshen ya lashi abu, akwai wani abu a saman bakinsu da ake kira Jacobson’s ko kuma Vomeronasal organ. Wannan ne ke baiwa maciji damar bin ganima sakamakon warin da suka bari a baya ko kuma ya nemi mata/miji
“Wannan na nufin idan har maciji zai ji wari sai dai ta baki ,” a cewar Kurt Schwent farfesa na illimin dangatakar halitta da muhallinsu da kuma sauyin halitta na jami’ar Connecticut.
Ko da shi ke, Sofrano ya ce ana iya hana macizai zuwa kusa da gidaje da muhallin da ke kewaye da su dan kaucewa hadarin da su ke da shi ga iyali, da dabbobin da ake ajiyewa a gida da ma muhalli.
“Banda tsabtace muhalli, babu wata hanyar da mutun zai iya hana macizai zuwa gidan. Hakan ya kunshi sharar gida da muhalli a bar ko’ina da sarari ta yadda ba zasu sami wani wurin buya ba. Dan haka a yanka ciyawa, a gyara Katanga da jinkan da suka bude. Ka da a rika zubar da shara a kasa da sauran abubuwan da ka iya kiran beraye ko abubuwan da macizan za su yi wa kallon abinci ko ganima. Yana da mahimmanci kuma a yi feshi a-kai- a-kai dan kariya daga macizan.
A Karshe
Babu wata hujjar da ta nuna cewa kona takarda cikin zuma na iya koran macizai. Warin ba shi da wani lahani ga maciji.