Cutar Korona ta kama wasu da ga cikin hadimai da ministocin shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Cikin waɗanda aka tabbatar sun kamu akwai kakakin fadar, Garba Shehu da babban sakataren fadar gwamnatin, Tijjani Umar. Sauran sun haɗa da ADCn Buhari, Yusuf Dodo da kuma da babban mai tsaron shugaban Kasa, Aliyu Musa.
Garba Shehu ya tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa lallai ya kamu da cutar bayan an dawo da sakamakon gwajin da aka yi ma sa.
Saidai kuma ya yi bayanin cewa yana cikin koshin lafiya, domin ko a lokacin da yake magana da PREMIUM TIMES ta waya ya ce yana wurin motsa jiki ne kamar yadda ya saba.
” An bani magunguna da nake sha, kuma Alhamdu lillahi ina cikin koshin Lafiya yanzu haka.
Shehu ta ce ba zai iya ci wa sauran albasa ba saboda bai san yawan waɗanda suka kamu ba.
Duk kokari da PREMIUM TIMES ta yi don taji daga bakin waɗanda ake zargin sun kamu da cutar wa ci tura, domin wayoyin su ba su shi.
Hadimin Buhari, Tolu Ogunlesi, ya bayyana wa wakilin cewa ba shi da masaniya game da waɗanda suka kamu da cutar a fadar shugaban kasa ya ce, kakain fadar gwamnatin ne kawai ya ke damar sanin komai kuma ya ɗa
Shima haka ministan Yaɗa labarai Lai Mohammed na daga cikin waɗanda ake zargin sun kamu da cutar.
Sai dai kuma majiya mai ƙarfi ta tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa minista Lai da sauran waɗanda suka kamu da cutar na killace a wani wuri ana duba su.
Idan ba a manta ba, a cikin wannan mako ne uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta sallami ma’aikatan ta dukkansu su tafi hutun dole har sai ta neme su.
Ko da yake bata bayyana dalilan yin haka ba, akwai raɗeraɗin cewa Korona ce ta sa aka tura ma’aikatan hutun dole har sai an neme su.
Discussion about this post