Ya Mai Martaba Sarki, wallahi har kullun, muna kara yiwa Allah Madaukakin Sarki godiya da yayi muna arzikin samun irin ka a cikin wannan mashahuriyyar al’ummah.
Wallahi duniya ta shaida, kuma babu mai tababa akan hakan, sai fa hasidin-iza-hasada, cewa duk bangaren da ka samu kanka a ciki na rayuwa, sai ka kyautatawa al’ummar ka, sai ka taimaki mutane, sai kayi wa yankin da ka fito na arewa hidima, sai kayi wa kasar ka hidima tsakanin ka da Allah, iya ikon ka, iya karfin ka.
Allah ya shaida, kuma bayin Allah ma sun shaida, a duk inda ka kasance, sai ka bayar da kyakykyawan jagoranci, da nuna jin kai da tausayi, tare da kusanta kanka ga talakawa; gami da tausayi da kyautatama al’ummarka, iya kokarin ka.
Wasu mutane basu sani ba saboda baka cika son a bayyana abubuwan da kake yi na alkhairi ba, saboda don Allah kake yi.
A lokacin da kake malamin makaranta, ka taimaka kowa ya sani. A lokacin da kake ma’aikaci a bankunan kasar nan daban-daban, wallahi ka taimakawa ‘yan kasuwa. Sannan ka zama sababi, kuma sanadiyyar yin arzikin mutane da yawa, domin kai Allah yayi ka ba mai hasada ba ne, ba mai ganin kyashi ba ne, sannan baka bakin cikin mutane su daukaka, ko su samu, ko su zama wani abu ta hanyar ka.
Sannan bayan Allah cikin ikon sa ya kaddari ka zama Gwamnan Babban Bankin kasar mu mai albarka, wato CBN; ka taimaki Najeriya daga durkushewar tattalin arziki a lokacin. Ka kwato hakkokan mutane da wasu azzalumai suka mayar mallakar su. Ka agazawa bankunan kasar nan daga durkushewa da kudin jama’ah. Ka taimakawa ‘yan kasuwa a Najeriya da arewa baki daya. Sannan babban al’amarin da ba zamu taba mantawa da kai ba saboda shi, shine, KAI NE SABABIN SAMAR DA BANKUNAN MUSULUNCI A KASAR NAN!
Abubuwan da kayi a lokacin da kake Gwamnan Babban Banki suna da yawa sosai. Wallahi ‘yan wadannan shafuka ba zasu isa in bayyana gudummawar da ka bai wa Najeriya, arewa, da al’ummar kasa ba. Sai dai kawai in tsaya iya nan saboda takaitawa.
Bayan nan, a lokacin da Allah ya dora ka akan gadon sarautar Kano mai albarka, wallahi Allah ne kadai yasan irin gudummawar da ka bai wa jihar Kano, da arewa, da Najeriya baki daya. Mu munyi imani, har ga Allah, cewa Babu wani mutum, ko shi wane ne, da zai iya kididdige amfanin da ka samar wa al’ummah, a lokacin da kake Kano. Shekaru shida da kayi, sun zama kamar shekaru dari shida akan karaga. Domin wallahi babu wani mutum da mace ta haifa, da zai iya mance wadannan shekaru shida masu albarka, tare da alkhairan da suka zo da su.
Wasu sun godewa kokarin da kayi, wasu kuwa sun butulce, ba domin komai ba sai domin hasada!
Kai ko su wadanda suka yi maka abunda suka yi maka, ba domin kayi wani laifi ba, a’a, sai dai saboda son zuciyar su, na tabbata, da za’a bincike su, tsakanin su da Allah, su fadi irin damuwar da suke ciki, saboda abun da suka yi maka na zalunci, da zaka tarar da cewa, abun yana nan yana damun su, kuma suna nan suna dana-sanin wannan ta’adi da sharrin da suka yi wa Kanawa, da Najeriya, da arewa, da ma duniya baki daya.
A yau, ta tabbata a fili karara, babu tababa, kai kace babu Sarki a Kano. Amma babu damuwa, mai hakuri yakan dafa dutse har yasha romon sa!
Yau kuma, ga shi nan, Allah Subhanahu wa Ta’ala, cikin ikon sa, da buwayarsa, ya dora ka akan wani babban matsayi, na shugabanci da jagorancin addini, wato Khalifancin darikar Tijjaniyyah. Muna addu’a da rokon Allah, yadda Allah ya baka iko da damar aiwatar da ayukkan alkhairi, a wadancan mukaman, to a nan ma Allah ya dafa maka, ya taimake ka, domin ka aiwatar da abubuwan da zasu zama alkhairi ga Musulunci da al’ummar Musulmi, da Najeriya da arewa, da ma duniya baki daya, amin summa amin.
Ya Khalifah, mu bamu da wani abu da zamu baka, illa sakayyar mu zuwa gare ka, da duk wani mutumin kirki, ita ce, mun dau alkawarin takarkarewa, wurin yi maka addu’o’i na kariya, da na dukkanin alkhairi, tare da rokon Allah yasa kaci nasara a duk yanayin da ka samu kan ka a ciki.
Domin a wurin mumini, babu abun da ya kai addu’a muhimmanci.
Bamu kadai ba, muna kira ga dukkanin masoya, ‘yan uwa da abokan arziki, da suma don Allah su zage damtse, suci gaba da yiwa Mai Martaba Sarkin Kano Khalifah Malam Muhammadu Sanusi II addu’a da rokon Allah a duk inda suke.
Kuma bayan nan, ina roko, don Allah, da mu da su baki daya, mu dage sosai wurin yiwa kasar mu Najeriya da yankin mu na arewa addu’o’i na musamman, domin samun zaman lafiya, da tsaro, da samun ingantaccen arziki da wadata.
Alhamdulillahi, da ma mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III yayi umurni da muyi Al-Qunuti, kuma muna nan muna yi da ikon Allah, har Allah ya tabbatar muna da nasara a kasar mu mai albarka, wato Najeriya!
Da fatan Allah ya albarkaci Mai Martaba Sarkin Kano Khalifah Malam Muhammadu Sanusi II; domin yaci gaba da taimakon addinin Allah, taimakon arewa, taimakon Najeriya, taimakon talakawa, taimakon bayin Allah marasa karfi, da nuna soyayya da kauna ga al’ummar sa. Sarki mutum ne da dole a jinjina masa.
Daga karshe, ina addu’a da rokon Allah, ya ba Sarki tsawon rai, da rayuwa mai albarka, mai amfani, domin ya ci gaba da taimakon addini da al’ummah, da taimakon arewa da ma Najeriya baki daya; domin samun dauwamammen zaman lafiya a arewa da ma kasa baki daya, amin.
Dan uwan ku: Imam Murtadha Muhammad Gusau, daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. 08038289761.