Gwamnan jihar Katsina Amjnu Masari ya maida wa gogarman ƴan bindiga Bello Turji da martani cewa bai isa ya saka wa gwamnati dokokin yin sulhu da shi.
” Turji a matasayin wa, ko kuma me, ayi sulhu da wa? Bai isa ya faɗi mana yadda za mu yi da shi ba. Wasikar sa ta neman sulhu ta banza
” Ya je ya nemi duka ƴan uwan waɗanda ya kashe ya nemi yin sulhu da su mana. Amma kuma don rashin kunya har saka wa gwamnati dokoki yin sulhu ya ke yi.
Idan ba a manta ba a cikin makon jiya Bello Turji ya aika wa gwamnati da doguwar wasika na kira ga mahukunta a zo a zauna a yi sulhu tsakanin sa da gwamnati.
A wasikar, Turji ya saka dokokin yin sulhu da shi, sannan ya yi alkawarin zai tabbatar babu wani ɗan bindiga da zai ci gaba da rike bindiga.
Ya ce zai kwace duka bindigogin da ke hannun ƴan bindiga ya mika wa gwamnati.
A baya dai gwamnatocin Katsina da Zamfara sun yi kokarin ayi sulhu da ƴan bindigan su dai kai hare-hare kan mutanen da basu ji ba basu gani ba amma hakan ya ci tura.
Maimakon a samu nasara da raguwar ta’addanci da suke gallaza wa jama’a, zafafa hare-haren yayi.
Daga nan kuma sulhu dai ya kife, aka kona gidan jiya inda daga karshe gwamnonin suka hakura da yin sulhun.
Discussion about this post