Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa za ta tsaurara matakai domin ganin mutane sun kiyaye dokar hana barace-barace, tallace-tallace da almajici a jihar.
Mashawarcin gwamnan kan harkokin yadda labarai Muyiwa Adekeye ya sanar da haka a wata takarda da aka raba wa manema labarai a farkon wannan makon.
Adekeye ya ce gwamnati na yi wa mutanen jihar tunin cewa akwai dokokin da ta saka domin kare hakin yara, hana dora wa yara kanana talla da bara a jihar na nan daram-dam.
Ya ce gwamnati ta kuma dora wa duba-garin dake hana acaba a jihar nauyin tabbatar da an kiyaye dokokin bara, talla da gararambar yara kanana a jihar.
Adekeye ya yi kira ga mutane da su bai wa wadannan duba gari hadin kai domin kare hakkin yara kanana a jihar.
Idan ba a manta ba a shekaran 2020 PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ya sa hannu kan Dokar Jihar Kaduna ta 2000, wadda aka yi wa kwaskwarimar hukuncin yi wa kananan yara fyade.
Sabuwar dokar ya tanadi dandake golayen namijin da ya yi lalata da kananan yara da kuma kassara al’aurar macen da ta yi fyaden kanramar yarinya ko yaro. Haka kuma akwai wuraren da dokar ta tanadi hukuncin kisa.
Bayan haka kuma, wadanda kotu ta yanke wa hukuncin za a rattaba sunayen su a Rajistar Masu Lalata Kananan Yara a Ofishin Antoni Janar na jihar da abin ya faru.
Dokan ya fara aiki ranar 11 Ga Satumba, ranar da El-Rufai ya sa wa dokar hannu.